Mage ta tara wa marasa galihu kudin taimako

Wata mage mai lakabin “Sir Whines-A-Lot” da aka cetota ta zama ’yar riko a ofishin Tulsa da ke Amurka ta rika karbo kudi daga jama’a masu wucewa tana kai wa gidan marasa galihu a wata cibiyar karkara. A Litinin din makon jiya ne hukumar kula da gajiyayyu ta bayyana shafinta na facebook cewa mage ta […]

Mage ta tara wa marasa galihu kudin taimako

Wata mage mai lakabin “Sir Whines-A-Lot” da aka cetota ta zama ’yar riko a ofishin Tulsa da ke Amurka ta rika karbo kudi daga jama’a masu wucewa tana kai wa gidan marasa galihu a wata cibiyar karkara.

A Litinin din makon jiya ne hukumar kula da gajiyayyu ta bayyana shafinta na facebook cewa mage ta tara kudi fiye da Dalar Amurka 100 a karshen mako, har ta kai ga kafafen yada labarai sun karkata kanta, kuma an baza labarinta a shafukan sada zumunta na intanet.

Masu magen sun fara neman taimako ga gidan gajiyayyu da marasa galihu cikin Agusta, lokacin da mutane suka fara wasa da kyanwar ta hnyar mika mata kudi a kafar kofar ofishin da take zaune, ita kuwa sai ta karbe kudin. Da kudin suka taru a gidan, masu ofishin sai suka yanke shawarar kai kudin gidan kula da marasa galihu.

 

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe

Yadda muke rayuwa bayan mutuwar mazajenmu —Matan sojoji