Magidanci ya bindige matarsa ya cinna wa dansa wuta
Magidanci ya bindige matarsa sannan ya banka wa gidansa wuta da dansa a ciki.
Wani magidanci ya bindige matarsa sannan ya banka wa gidansa wuta da dansa a ciki.
Dan nasa mai shekara 29 ya rasu a gobarar, yayin da ake ci gaba da alhinin abin da magidancin ya aikata da misalin karfe 3 na asubahi.
- Yadda ’yan bindiga suka karkashe juna a Katsina
- Sojoji mata 200 za su yi sintiri a hanyar Abuja-Kaduna
- ’Yan bindiga sun kai hari mahaifar Shugaban Majalisar Zamfara
Bayan mutuwar matar da dan nasa, sai ya mutumin mai shekara 65 wanda kuma mafarauci ne ya kashe kansa da bindigar.
Wani shugaban ’yan banga ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar lamarin a Karamar Hukumar Awka ta Arewa ta Jihar Anambra a safiyar Alhamis.
Kakakin ’yan sandan Jihar, CSP Haruna Mohammed, ya ce abin ya faru ne a unguwar Amunike, kuma “har yanzu ba a gano abin da ya sa muutumin yin hakan ba.”
Ya ce bayan ’yan sanda masu binciken kwakwaf daga yankin Achalla sun isa wurin, sai suka kai mutanen asibiti inda likita ya sanar cewa sun riga sun mutu.
A cewarsa, ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.