Magidanci ya caka wa matarsa wuka a kotu a Kano

Sai da ’yan sanda suka yi harbi kafin su shawo kan magidancin.

Magidanci ya caka wa matarsa wuka a kotu a Kano

Wuka

Wani magidanci ya caccaka wa matarsa da ke dauke da juna biyu wuka a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano.

Magidancin ya zaro wuka ya rika caccaka wa matar da wanta ne bayan  zaman kotun da ta kai kara kuma alkali ya raba aurenta da tsohon mijin nata.

Matar ta ce ta nemi kotun Musuluncin da ke zamanta a Karamar Hukumar Rano da ta raba aurenta da tsohon mijin nata ne saboda yana hana ta abinci, yana kuma cutar da ita.

Matar mai suna Shafa’atu Sale ta ce, “Alkali ya ce in ba shi sadakinsa N20,000 amma ya ki karba, sai ya karba a hannun [dan uwana] Ado.

“Da muka fito daga kotu shi ne ya dinga bin mu, sannan ya zaro wuka ya fara caka wa Ado a ciki ni ma ya rika caka min.”

Da yake kwatanta abin da ya faru, wan matar mai suna Ado ya ce  da kyar ’yan sanda suka kwace shi da kanwarsa a hannun tsohon mijin nata.

Ya ce tsohon mijin kanwar tasa “ya biyo mu ta baya ya caka min wuka a cikina da sauran sassan jikina.

“Da kyar na ruga da gudu zuwa bakin kotu; ban yi zaton zai caka mata wukar ba.

“Shi ne ’yan sanda suka zo su ma da kyar suka kama shi, sai da suka harba bindiga.”

Kano Focus ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba