Magidanci ya kashe agola don ya samu soyayyar amaryarsa

Ana zargin wani magidanci mai kimanin shekara 40 da kashe agolansa mai shekaru 17 domin samun soyayyar amaryarsa, mahaifiyar yaron. Lamarin da ya auku a kauyen Tsakuwama a Karamar Hukumar Miga da ke Jihar Jigawa ya sanya al’ummar yankin cikin zullumi. ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Abuja Bashin da ke bin Najeriya […]

Magidanci ya kashe agola don ya samu soyayyar amaryarsa

Ana zargin wani magidanci mai kimanin shekara 40 da kashe agolansa mai shekaru 17 domin samun soyayyar amaryarsa, mahaifiyar yaron.

Lamarin da ya auku a kauyen Tsakuwama a Karamar Hukumar Miga da ke Jihar Jigawa ya sanya al’ummar yankin cikin zullumi.

Kakakin rundunar tsaro NSCDC a Jihar Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce a ranar 14 ga watan Agustan 2020, wanda ake zargin ya tafi gona tare da agolansa mai suna Adamu Gambo dan matar da yake aure, ya kashe shi a gonar.

Ya ce Jami’an hukumar NSCDC sun tsare wanda ake zargin ya kuma amsa laifinsa na kashe agolan nasa.

Adamu ya kara da cewa wanda ake zargin ya ce ya kashe yaron ne saboda yana dauke hankalin mahaifiyarsa daga gare shi, wanda hakan yake hana shi samun cikakkiyar soyayyarta.

Don haka ya kashe yaran domin ya samu cikakkiyar soyayya daga amaryarsa.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo