Magidanci ya kashe kansa saboda rashin albashin watanni 13
Wani maaikaci da ke aiki da Hukumar Ruwa ta Jihar Bayelsa, Peter Ogiero ya rataye kansa saboda rashin biyansa albashin watanni 13 da hukumar ta yi.Aminiya ta kalato cewa tun da aka samu jinkirin biyan albashi sai ya fara kamuwa da cutar hawan jini, daga nan kuma shanyewar baryar jiki ta kama shi; duk dai […]
Wani maaikaci da ke aiki da Hukumar Ruwa ta Jihar Bayelsa, Peter Ogiero ya rataye kansa saboda rashin biyansa albashin watanni 13 da hukumar ta yi.
Aminiya ta kalato cewa tun da aka samu jinkirin biyan albashi sai ya fara kamuwa da cutar hawan jini, daga nan kuma shanyewar baryar jiki ta kama shi; duk dai saboda zullumin yaushe za a biya albashi. Haka nan kuma ganin ya shiga tsaka mai wuya saboda nauyin iyali da sauran hidima ta yau da kullum, abubuwa sun tsaya masa, sai Mista Ogiero ya yanke shawara ba tare da sanin kowa ko shaida wa kowa haka ba, ya kwankwadi maganin kwari, abin da kuma ya yi sanadin ajalinsa.
Da take yi wa manema labarai karin haske game da lamarin, ’yar uwar mamacin, Teena, ta ce dan uwanta ya shafe wata 12 yana fama da cutar shanyewar barin jiki, lokacin da suka tafi sawo masa abincin da zai kalaci, ya sha maganinsa; koda suka shigo gida sai suka iske shi yana malelekuwa, yana kakatun mutuwa. Kafin a yunkura a kai shi asibiti ya ce ga garinku nan.
Iyalai da dangin mamacin sun dora alhakin mutuwar dan uwan nasu kan rashin biyan albashin wata 13 da gwamnatin jihar ta ki yi.