Magidanci ya kashe kansa ya bar matarsa da tsohon ciki
Matsafa sun yanki gawar mutum da aka tsince ta tana lilo a jikin bishiya.
Wani magidanci mai shekara 45 ya rataye kansa ya bar matarsa da tsohon ciki.
Kakakin ’yan sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata a unguwar Oke-Opo da ke Ilesa a Jihar.
- An kone wanda ake zargi da satar babura kurmus a Osun
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
- Sai da na kusa kashe kaina saboda talauci – Tsohon dan kwallon Arsenal Eammnuel Eboue
Mamacin wanda tela ne ya bar gida tun ranar Litinin ba tare da ya sanar da matarsa mai tsohon ciki ko wani inda za shi ba.
Mutanen yankin sun tsinci gawar Olatunji tana lilo ne a jikin wata bishiya.
Ana zargin matsafa sun yanki wani bangare na jikin mamacin kafin su sauke gawar daga kan bishiyar.
Wani matsafi a yankin da ya nemi Aminiya ta sakaya sunansa ya ce dole ne a yanki wani bangare na jikin gawar don guje wa faruwar wani bala’i da ka iya tasowa a gaba.