Magidanci ya kashe mahaifiyarsa a Neja
Mahaifiyar ta gamu da ajalinta yayin da ta rabun fada tsakanin danta da mai dakinsa.
Wani magidanci ya caka wa mahaifiyarsa wuka ya aika ta lahira sannan ya yi wa matarsa rauni da wukar.
Matashin, mai shekara 27, ya aikata danyen aikin ne bayan wani sabani da suka samu da matar tasa a garin Kontagora na Jihar Neja.
- Sauye-sauyen da Majalisar Tarayya ta yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999
- NATO ta zargi Putin da tayar da zaune tsaye a Turai
Shaidu sun ce ya luma wa mahaifiyar tasa wuka ne bisa kuskure a lokacin da dattijuwar take kokarin raba fada tsakaninsa da matarsa a yayin da ma’auratan suke ba wa hamata iska.
Matar tasa da ya yi wa raunuka da wukar kuma an kai ta Babban Asibitin Kontagora domin jinyar ta.
Wata majiya da wakilinmu ya zanta da ita, ta bayyana a sirrance cewa matashin da ya yi aika-aikan yana fama da tabin hankali.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Bala Kuryas ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ana gudanar da bincike a kai.