Magidanci ya kashe matarsa da dansa
Mutum ya yi wa iyalan nasa mummunan kisa
Wani magidanci mai ya kashe matarsa da dansa mai shekara hudu ta hanyar amfani da shebur.
Majiyar Aminiya ta ce magidancin ya hallaka matarsa da dan nasa ne ta hanyar bubbuga musu shebur din da ya yi amfani da shi a kai.
- Buhari ya gana da sabbin Hafsoshin Tsaro
- An cafke shi ya kashe mahaifiyarsa da ’ya’yansa
- ’Yan sanda sun kama wanda ya kashe mahaifinsa
- Kotu ta ba mayu awa 24 su warkar da mara lafiya
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Anmabra, CSP Haruna Mohammed, ya ce “mutumin ya farmaki matarsa da dansa mai shekara hudu, ya buga musu shebur a kai.”
Mutumin ya kuma yi amfani da shebur din wajen kai farmaki wa wani dan banga kafin daga baya a kama shi.
CSP Haruna ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, ‘yan sanda sun garzaya da matar da yaron zuwa asibitin Ozubulu, ina likita ya sanar da cewa sun mutu.
Jami’in ya kuma bayyana cewa dan bangar da mutumin ya farmaka da shebur na murmurewa a asibiti.
Ya ce abin alhinin ya faru ne a kauyen Ofufe Nza a Karamar Hukumar Ekwusigo, da ke Jihar ta Anambra, inda jami’an Rundunar suka cafke wanda ake zargin a ranar Talata da misalin karfe 7:45.
Sai dai kuma ya kara da cewa ana zargin cewa magidancin da ya yi danyen aikin na fama da tabin hankali.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP John Abang, ya ba da umarnin a ci gaba da binciken wanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka na Rundunar domin gano abin da ya faru.