Magidanci ya kashe matarsa da tsohon ciki a Enugu
Wani magidanci mai suna Ozoemena Nwankwo ya yi wa matarsa Ndidi Nwankwo mai tsohon ciki dukan kawo wuka a kauyen da suke zaune na Akpawfu, da ke karamar Hukumar Nkanu ta Gabas Jihar Enugu, har sai da ta ce ga garinku nan. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Enugu, Ebere Amaraizu ne ya […]
Wani magidanci mai suna Ozoemena Nwankwo ya yi wa matarsa Ndidi Nwankwo mai tsohon ciki dukan kawo wuka a kauyen da suke zaune na Akpawfu, da ke karamar Hukumar Nkanu ta Gabas Jihar Enugu, har sai da ta ce ga garinku nan.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Enugu, Ebere Amaraizu ne ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya shiga hannu.
“Gawar matar tasa yanzu haka an ajiye ta a wani asibiti da ke Agbani, shi kuma wanda ake zargi da aikata laifi Nwanko ya shiga hannu,” a cewar Kakakin ’yan sandan.
Za a iya bayyana lamarin da fargar jaji, inji dan sandan,domin “sai yanzu ne ya nuna nadama kan abin da ya aikata, har ma yake cewa shi bai yi tsammani matar tasa dukan zai kai ga ajalinta ba.”
Wata majiya da ke makwabtaka da Ozoemena Nwankwo, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa Aminiya cewa “dabi’arsa ke nan dukan matar, laifi kadan ba shi da hakuri sai ya hau lakada wa matar duka, kuma tana da tsohon ciki ma ya doke ta, har sai da ta fadi somammiya,” inji majiyar.