Magidanci ya koma mace a asibitin kasar Sin

Wani magidanci a kasar Sin dan shekara 44, da ke zaune a yankin Zhejiang ya je wurin likita don a duba shi kan matsalar ciwon ciki da ta addabe shi, da jini da ke gudana a fitsarinsa, sai kawai aka gano cewa a she shi mace ne, kuma yana yin jinin al’ada a lokacin. Baya […]

Magidanci ya koma mace a asibitin kasar Sin
Magidanci ya koma mace a asibitin kasar Sin

Wani magidanci a kasar Sin dan shekara 44, da ke zaune a yankin Zhejiang ya je wurin likita don a duba shi kan matsalar ciwon ciki da ta addabe shi, da jini da ke gudana a fitsarinsa, sai kawai aka gano cewa a she shi mace ne, kuma yana yin jinin al’ada a lokacin. Baya ga wannan likitoci sun gano cikakkiyar halitta mahaifar mace a cikinsa.
Shugaban asibitin First People da ke Yongkang ba su taba tsammanin Chen mace ce ba. “Yana sanye da kayan maza, ga shi ya yi aski irin na maza, don haka ba mu taba tunanin shi mace ce ba,”  acewarsa, amma da muka tsananta bincike sai muka gano cewa al’aurarsa ta sha bamban da ta suaran maza, kuma ba shi da tsinin makogwaro.
Irin wadannan al’amura na dadewa ba su auku ba, musamman a wajen bincike da nazarin likitanci. Likitoci sun bayyana cewa lokaci ya kure ga Chen ballantana ya nemi magani, domin ana iya juya shi zuwa cikakken namiji da an gano matsalar tun yana dan karami.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe