Magidanci ya kona agolansa da dutsen guga

Wani magidanci mai suna Mista Kunle Anisere da ke zaune a birnin Ibadan, ya yi wa agolansa dan shekara 12 mummunan rauni ta hanyar goga masa dutsen guga mai zafi a sassan jikinsa saboda bacewar da Naira dubu daya  daga hannunsaAgolan mai suna Azeez Yusuf, yanzu haka ’yan sanda a Jihar Oyo sun kama magidancin […]

Magidanci ya kona agolansa da dutsen guga
Magidanci ya kona agolansa da dutsen guga

Wani magidanci mai suna Mista Kunle Anisere da ke zaune a birnin Ibadan, ya yi wa agolansa dan shekara 12 mummunan rauni ta hanyar goga masa dutsen guga mai zafi a sassan jikinsa saboda bacewar da Naira dubu daya  daga hannunsa
Agolan mai suna Azeez Yusuf, yanzu haka ’yan sanda a Jihar Oyo sun kama magidancin don masa tambayoyi kafin a kai shi kotu.
Wakilinmu, ya jiyo tabbatattun bayanai daga kowane bangare har da Kunle Anisere wanda bai musanta abin da ake zargi ya aikata ba, da jin ta bakin matarsa  Toyin Anisere da ta yi bayani dalla-dalla  game da aukuwar al’amarin.
 Wata malama (an sakaya sunanta) da ke koyarwa a aji 4 na makarantar da yaron ke zuwa , ita ce ta bankado halin tagayyara da dalibinta Azeez Yusuf yake ciki a dalilin raunuka a kirjinsa da kafadarsa,  inda yaron da kansa ya gaya mata dalilin raunukan da ke sassan jikinsa. Ita kuma ta garzaya zuwa ofishin ’yan sanda ta kai rahoto. Nan take Babban Jami’in ’Yan sanda CSP John Aku, ya aiki jami’ansa su kamo Mista Kunle Anisere da matarsa wato mahaifiyar yaron Uwargida Toyin Anisere domin jin dalilin da ya sa suka aikata wannan danyen aiki.
Da yake fadin abin da ya haifar da raunuka a jikinsa, Azeez Yusuf ya ce: “A kowane lokaci na dawo daga makaranta, ina yi wa mahaifiyata tallar kifi har zuwa wannan rana da Naira dubu daya suka bace daga cikin aljihuna. Mahaifiyata ta yi mini dukan tsiya. Kashegari sai na wuce gida kai-tsaye daga makarata na ki komawa shagonta,  inda mijinta ya kulle ni a cikin gida ya yi ta dukana. A lokacin da ya ga ban yi kuka ba, sai ya dauko dutsen guga ya makala a wutar lantarki ya yi zafi ya kama gogawa a jikina saboda haushin bacewar wannan kudi.”
Da aka nemi jin ta bakinsa, Mista Kunle Anisere da ke sana’ar acaba ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga yin wannan hukunci: “Domin yau shekara 3 ke nan da nake kula da tarbiyyar wadannan yara biyu, ’ya’yan matata da ta haife su da tsohon mijinta, ban taba dukansu da sunan hukunci ba; domin kada makwabta su ce ina tursasa musu ne saboda ba ’ya’yana ba ne.”
Ita kuwa mahaifiyar yaron, uwargida Toyin Anisere ta yi dogon bayani ne a kan yadda ’ya’yanta biyu Azeez da yayansa Ibrahim suka durkusar da harkokin kasuwancin da take yi, don biya musu kudin makaranta da bukatun yau da kullum. Sai dai ta yi mamakin irin hukuncin da mijinta ya yi wa Azeez, wanda ta ce: “Ina kyautata zaton aikin Shaidan ne da yake so ya jefa mu cikin damuwa.”b