Yadda magidanci ya mutu garin ceton tunkiya

Wani magidanci mai shekara 55 ya gamu da ajalinsa a kokarinsa na ceto tunkiyarsa da ta fada rijiya. Lamarin da ya faru a kauyen Sha’iskawa a Karamar Hukumar Dambatta ta Jihar Kano ya jefa al’ummar yankin cikin zullumi. Marigayin mai suna Abdul-Hamid Muhammad ya yi kokarin ceto tunkiyar da ta fada rijiyar ne bayan da […]

Yadda magidanci ya mutu garin ceton tunkiya

Wani magidanci mai shekara 55 ya gamu da ajalinsa a kokarinsa na ceto tunkiyarsa da ta fada rijiya.

Lamarin da ya faru a kauyen Sha’iskawa a Karamar Hukumar Dambatta ta Jihar Kano ya jefa al’ummar yankin cikin zullumi.

Marigayin mai suna Abdul-Hamid Muhammad ya yi kokarin ceto tunkiyar da ta fada rijiyar ne bayan da ya shiga cikin rijiyar ya fita daga hanyyacinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Sa’idu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an yi kokarin ceto rayuwar mamacin, aka kai shi Babban  Asibitin garin Dambatta, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

“A ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2020 da misalin karfe 4:37 na yamma wata mace mai suna Ummu Muhammad da ke kauyen na Sha’iskawa ta sanar mana da faruwar lamarin ta wayar salula.

“Jami’anmu sun isa wajen inda suka iske mutumin mai suna Abdul-Hamid Muhammad wanda ya fada rijiya

“Bayan mun fito da shi daga rijiyar mun garzaya da shi Babban Asibitin garin Dambatta inda likitoci suka tabbatar ya rasu”, inji shi.

NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar