Magidanci ya rasu wajen ceto ɗansa a rijiya
Mutumin ya rasu wajen ceto ɗansa da ya fada rijiya.
Wani magidanci mai suna Fasasi AbdulAfeez, ya rasu yayin ceto ɗansa da ya fada rijiya a Jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a kauyen New Maselu, Gaa Jangbo da ke Karamar Hukumar Offa a jihar.
- Askarawan Tsaro: Wasiƙa zuwa ga Gwamnan Zamfara
- Za mu sa kafar wando da masu ambato juyin mulki — Sojoji
Dan mutumin mai suna Khaleed, dan shekara 17 ya fada rijiya ne lokacin da ya je debo ruwa.
Yaron ya zame ya fada rijiyar ne, wanda hakan ya sa mahaifinsa kai masa dauki.
Lamarin ya ja hankalin mazauna yankin, wanda hakan ya sa suka kira Hukumar Kashe Gobara ta jihar, don ceto shi.
Kakakin hukumar, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu kiran waya ne daga wani mutum mai suna Alhaji Taiye Gadamosi da ke zaune a unguwar.
A cewarsa, “Lamarin ya faru da misalin karfe 4:11 na yammacin ranar Alhamis.
“An dauko gawar mutumin daga cikin rijiyar. Yaron mutumin ya farfado bayan dogon suma,” in ji shi.
Adekunle ya kara da cewa “Shugaban hukumar, Prince Falade Olumuyiwa, ya bayyana bakin cikinsa kan faruwar lamarin.
“Ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, sannan su guji tura yara debo ruwa a rijiya,” in ji shi.