Magidanci ya rataye kansa a Adamawa

Wani magidanci mai ’ya’ya uku mata ya rataye kansa a yankin Jimeta da ke Jihar Adamawa

Magidanci ya rataye kansa a Adamawa

Gawa

Wani magidanci ya rataye kansa a yankin Jimeta da ke Jihar Adamawa.

An tsinci gawar magidancin da ake zargin ya rataye kansa ne a gidnasa da ke kusa da ke garin.

Wasu shaidu sun ce mutumin yana zaune tare da ’ya’yansa mata uku ne a cikin wani kango, tun bayan rabuwarsa da matarsa shekaru uku da suka gabata.

Zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto dai hukumomin jihar ba su ce komai kan lamarin ba.

Amma dai an dauke gawar zuwa dakin ajiyar gawa kafin a yi mata jana’iza.

Karo na biyu ke nan da mutane suka kashe kansu a unguwar a cikin ’yan kwanakin nan.

A kwanakin baya wata ma’aikatar lafiya mai shekara 22 a yankin ta kashe kanta bayan rasuwar saurayinta a yankin.

Dangote ya karya farashin man fetur

An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati

Matasa 150 Sun Halarci Gasar Kirkire-Kirkiren Fasaha a Kano

APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar