Magidanci ya saki matarsa don ta ki daukar sakon wayarsa na WhatsApp

Wani mutum a kasr Saudiyya ya saki matarsasabodaba takula da sakona WhatsApp.Duk da cewa tana yawan amfani da wayar salularta, jaridar GulfNews ta ruwaito cewa, matar ba ta mayar da amsar sakon mijinta ba. Wadannan ma’aurata dai sun kasance tare da juna tsawon shekara biyu. Mijin wannan mata dai ya harzuka ganin cewa ta dukufa […]

Magidanci ya saki matarsa don ta ki daukar sakon wayarsa na WhatsApp
Magidanci ya saki matarsa don ta ki daukar sakon wayarsa na WhatsApp

Wani mutum a kasr Saudiyya ya saki matarsasabodaba takula da sakona WhatsApp.Duk da cewa tana yawan amfani da wayar salularta, jaridar GulfNews ta ruwaito cewa, matar ba ta mayar da amsar sakon mijinta ba. Wadannan ma’aurata dai sun kasance tare da juna tsawon shekara biyu.

Mijin wannan mata dai ya harzuka ganin cewa ta dukufa wajen yawan amfani da wayar salularta. Ya yi ikrarin cewa, ta yi watsi da kula da gida da yara.
Ita kuwa wannan mata ta ce, tana bukatar wayar salulrta don hulda da kawaye da ’yan uwa. Da takaici ya ishi wannan miji, sai ya yi amfani da hanyar sadarwatawhatsApp, don ya yi magana da ita, sai ta yi watsi da sakonninsa, saboda kawai ta dukufa wajen hira da kawayenta.