Magidanci ya shekara goma da ciwon kafa

dan kasuwa, dan asalin Jihar Kano, Alhaji Bashir Badamasi, mazaunin Legas ya bayyana cewa shekararsa goma cur yana dauke da ciwon kafa, sakamakon karayar da ya samu a 2006.Macinyacin, dan shekara 65 a duniya, ya ce ya kwashe fiye da shekaru 40 yana zaune Legas, inda yake gudanar da kasuwancinsa na sayar da barkono. Ya […]

Magidanci ya shekara goma da ciwon kafa
Magidanci ya shekara goma da ciwon kafa

dan kasuwa, dan asalin Jihar Kano, Alhaji Bashir Badamasi, mazaunin Legas ya bayyana cewa shekararsa goma cur yana dauke da ciwon kafa, sakamakon karayar da ya samu a 2006.
Macinyacin, dan shekara 65 a duniya, ya ce ya kwashe fiye da shekaru 40 yana zaune Legas, inda yake gudanar da kasuwancinsa na sayar da barkono. Ya bayyana cewa, a sanadiyyar jinyar wannan kafa, al’amuransa kusan komai ya tsaya cik.
Ya bayyana wa Aminiya cewa, ya fara gamuwa da wannan larura ce a shekarar 2006; a kan hanyarsa ta zuwa kasuwancinsa. Ya ce ya fadi ne a wata magudanar ruwa, wanda hakan ya yi sanadiyar karyewarsa a cinya. Bayan an gyara karayar a wancan lokacin sai kuma wata mota ta kara buge shi a daidai karayar.
“An kai ni asibiti domin gyaran karayar amma asibitin sun bukaci Naira dubu 538,700 domin a yi mini aiki. Ni kuma wallahi karfina ya kare. Abin da nake da shi a hannu bai wuce Naira 200,000 ba. Matata da take taimaka mini da kuma daukar dawainiyar yara; Allah Ya yi mata rasuwa. Kowa ya sani, karfina ya kare. Yanzu ba na iya yin komai, a kodayaushe ina nan a masallacin Juma’a da ke unguwar Idi-Araba, Legas.