Magidanci ya sumar da kanwarsa bazawara a kan dan mangwaro
Wata bazawara mai suna Huwaila Abubakar Maibindiga da take zaune a Gidan Narabi a kauyen Kugu da ke Gundumar Dutsen Abba, a karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna ta samu kanta a gadon asibiti a dalilin dukan da dan uwanta ya yi mata saboda ta tsinki dan magwaro. Aminiya ta ziyarci Asibitin Nura da ke Kamfani […]

Wata bazawara mai suna Huwaila Abubakar Maibindiga da take zaune a Gidan Narabi a kauyen Kugu da ke Gundumar Dutsen Abba, a karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna ta samu kanta a gadon asibiti a dalilin dukan da dan uwanta ya yi mata saboda ta tsinki dan magwaro.
Aminiya ta ziyarci Asibitin Nura da ke Kamfani Saye a garin Dutsen Abba, inda ta tarar da bazawarar kwance a gadon asibiti tana jinya, ta shaida wa wakilinmu cewa: “A ranar Asabar da misalin karfe uku na rana bayan na gama wa matan yayyena kitso sai na hangi wani dan magwaro nunan ne a sama sai na ce ga wani magwaro can a sama nunanne. Sai na dauko makata zan tsinko, ina tsinkowa sai kawai ya fado a kan kwano sai yayana mai suna Isa ya fito ya hauni da bugu, har ma da karo duk ya farfasa min baki nan take na suma ban ma san an kawo ni asibiti ba sai bayan wani lokaci.”
Huwaila ta kara da cewa, “Mahaifimmu daya, uwa kowa da tasa, kuma da ma ba sa kaunar ’yan dakinmu suna nuna mana ’yan ubanci kwarai da gaske tun ba yau ba, muna zaman hakuri ne da ’yan dakinsu a dakinmu, mu biyu ne kawai, kuma dukanmu mata ne, muna hakuri da su akan irin abin da suke yi mana, suna cewa wai mahaifinmu ya fi sonmu.”
Huwaila ta ce, abin da ya sa ta dawo gidan da zama shi ne Allah Ya yi wa mijinta rasuwa. “Da ina gidan mijina ne ai ba zai gan ni ba har ya yi min haka, na yafe masa tunda Allah Ya sa ban mutu ba, kuma idan na sake samun miji aure zan yi,” inji ta.
Daraktan Asibitin Dokta Muhammed Nura Hashim ya ce da misalin karfe hudu na yamma ’yan sanda suka kawo ta asibitin tana cikin wani yanayi mara kyau don haka suka fara kula da ita, kuma Allah cikin ikonSa Ya ba ta lafiya. Ya ce irin wannan duka na rashin hankali bai dace a ce mutum mai iyali yana irinsa ba.
Mahaifinsu, Malam Abdullahi Maibindiga ya nuna bacin ransa a kan abin da dan nasa ya yi, kuma ya ce da ma ya sha ja musu kunne a kan irin kiyayyar da ya ce suna nuna wa ’yan uwan nasu. Ya ce ai wanda ya yi dukan ne ya shuka mangwaron ba kuma gidan ba shi ya gina ba, don haka idan hukuma ba ta dauki mataki mai tsauri ba, to shi zai dauki irin abin da ya ga ya dace da kansa don ganin haka bai sake faruwa a gidansa ba.
Aminiya ta tuntubi babban jami’in ’yan sanda na ofishinsu da ke danmagaji, Buhari Bello inda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun kama wanda ya yi wa matar duka yana hannunsu suna jiran sakamakon asibiti kafin su dauki mataki na gaba.