Magidanci zai shekara 400 a kurkuku saboda yi wa agolarsa fyade sau 900
Magidanci mai shekara 46 ya yi wa yarinya mai shekara 10 fyade kusan sau dubu
Kotu ta kama wani magidanci mai shekara 46 da laifin yi wa yarinya mai shekara 10 fyade kusan sau dubu a tsawon akalla shekara biyar.
An gurfanar da mutumin ne a gaban babbar kotun Durban da ke Afirka ta Kudu a ranar Juma’a 26 ga watan Maris 2021.
- Ba zafin kai kuka fi mu ba —Matawalle ga ’yan Kudu
- Matar aure mai sana’ar tuka Keke NAPEP a Kano
- Sarkin Zazzau ya tumbuke rawanin Ciroman Zazzau
- Mai garkuwa da mutane ya nemi ya kashe kansa bayan an ritsa shi
Da farko, kotun ta yanke masa daurin shekara 176 a gidan yari ne bayan samun sa da laifuka 56 masu alaka da laifin yin fyade, safarar yara da yin kwalliyyar jima’i da cin zarafin mata da kuma raba hotunan tsiraicin yara.
Jaridar The Sunday Times Daily ta ruwaito mutumin ya yi amfani gubar acid wajen kone dan yatsar da za a iya gano wasu laifuka masu alaka da ake zargin sa da aikatawa.
An kama shi ne a watan Yuni a shekarar 2018 a garinsu da ke Berulam a Arewacin Durban, bayan yarinyar ta fallasa badalar da ya yake aikatawa.
Sai makwabtan mutumin cikin ayarin mata suka tuntube shi bayan dawowarsa gida daga wajen aiki.
An tuntubi jami’an kamfanin tsaro na Reaction Unit SA (Rusa) inda suka sanar da kakakin jami’an mai suna Prem Balram wanda ya ce, matan sun bukaci taimakonsa bayan sun fallasa wani bidiyo da ke nuna lokacin da mutumin yake yin fyade da aka gano a cikin wayar sadarwarsa.
“An samu wasu bidiyoyinsa lokacin da yake yi wa wasu mata fyade da wasu bidiyon wasu maza suna yi wa wasu yara mata fyade duk a cikin wayar salular wanda ake zargin. An kuma samu hotunan dan kamfai na matan da ake zargin yana yin badala da su.’’
A lokacin shari’ar, an da laifin yi wa ’yar matarsa fyade tun bayan rasuwar mahaifiyar yarinyar a shekara 2013 a kusan kowane lokaci a rana a gidajensu da ke yankunan Benoni da Effingham da Pinetown da Reserboir Hills da Sydenham da kuma wasu yankunan Gauteng da Kwazulu-Natal.
Alkalin kotun Mohini Moodley ya samu mutumin da laifuka 56, sannan za a yi rijistar sa a matsayin mai laifin yin fyade.
Mai laifin yin fyaden zai yi zaman kaso na kusan shekara 400 a gidan yari na Durban’s Westbille Correctional Centre.