Magidanta 340 sun sha duka a hannun matansu a Legas
Nau’ikan matan da ke duka mazajensu da kuma dalilai
Gwamnatin Legas ta ce a cikin shekara daya, daga watan Satumban 2022 zuwa Yulin 2023 magidanta 340 ne matansu suka yi wa dukan kawo wuka a Jihar Legas.
Gwamnatin ta nuna damuwa dangane da karuwar yawan mazan da matansu suke dukan su a duk lokacin da rashin jituwa ta samu a tsakaninsu.
Gwamnatin ta ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa a takaice a cikin shekara daya, daga watan Satumban 2022 zuwa Yulin 2023 an samu rahotannin maza 340 da matansu suka yi wa dukan kawo wuka a Jihar Legas.
Babbar Sakataren hukumar yaki da cin zarafi da cikin gidade ta jihar (DSVA) Uwargida Titilola Vivour-Adeniyi ce ta fadi haka cikin rahoton da hukumar ta saba fitarwa duk bayan watan uku.
- Budurwa ta mutu tana tsaka da saduwa da ‘Dan Yahoo’
- Jirgi ya jefa wa masu taron Mauludi bom a Kaduna
Nau’ikan mata masu duka miji
Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan yadda za a shawo kan yadda mata ke dukan mazajensu, wani magidanci, Bala Maijarida ya ce “zai yi wuyar gaske a iya yin maganin aukuwar irin wannan matsala domin nau’in matan da suke dukan maza sun kasu kashi-kashi ne.
“Akwai masu takama da kudin da suke ba mazansu jari da suke tilasta mazan yin abun da suke so, musamman idan jarin ya karye.
“Hakan ne yake sa wasu mata daukar irin wannan matakin dukan maza domin ladabtarwar.
“Akwai kuma mata masu takama da gidan da suka mallaka da suke yin barazanar korar miji daga gidan idan ya kasa bin umarninsu.
“Sai kuma nau’in fitinannun mata da wannan lamari ya shiga cikin jinin jikinsu da ba za su iya barin fitinar tasu ba.
“Kuma akwai mata mashaya abubuwan maye da suke amfani da wannan dama wajen tursasa wa miji.
“Saboda haka zai yi wuyar gaske a iya yin maganin aukuwar irin wannan lamari a Jihar Legas.”
Alhaji Bala Maijarida ya ce, “Ba safai ake samun mata masu dukan mazajensu a cikin al’ummar Hausawa mabiya Islam ba.”