Magidanta biyu sun yi wa ‘yar shekara 9 fyade a Nasarawa
Ana zargin wasu magidanta biyu da yi wa wata karamar yarinya ‘yar kasa da shekaru 9 fyade a Lafiya na Jihar Nasarawa ranar Larabar da ta gabata. Wakilinmu ya ziyarci inda lamarin ya auku, kuma ya gana da wani daga cikin matasan da suka kamo wadanda suka aikata laifin mai suna Mustapha Musa, inda ya […]
Ana zargin wasu magidanta biyu da yi wa wata karamar yarinya ‘yar kasa da shekaru 9 fyade a Lafiya na Jihar Nasarawa ranar Larabar da ta gabata.
Wakilinmu ya ziyarci inda lamarin ya auku, kuma ya gana da wani daga cikin matasan da suka kamo wadanda suka aikata laifin mai suna Mustapha Musa, inda ya bayyana cewa bayan sun kamo wadanda ake zargin sun yi musu wasu tambayoyi kafin su kai su ofishin jami’an hukumar Cibil Defence.
Matashin ya ce magidantan sun tare karamar yarinyar ce mai suna Fatima Haruna a lokacin da take wucewa sai daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Abdullahi Aliyu mai kimanin shekaru 43 bayan ya tsaida ita sai ya lallabeta cewa ta biyo shi zuwa cikin wani tsohon gini da ba a kammala ba zai bata kyautar naira 200 da takalmin roba.
Ya ce, Nan take sai ta bi shi cikin ginin, inda ya yi mata fyade. Bayan ya aikata danyen aikin ne sai ya kuma rude ta cewa ta jira shi a ginin zai fita ya je ya sayo mata takalmin kamar yadda ya yi mata alkawari. Daganan sai ya je ya sanar wa wannan abokin nasa mai suna Nura Ahmed mai kimanin shekaru 37 abin da ya aikata, ya kuma gaya masa cewa idan shi ma yana bukatar yin haka zai kai shi inda yarinyar take.
“Da jin haka sai Nura Ahmed bai yi wata-wata ba ya bi abokin nasa ya kai shi tsohon ginin inda shi ma ya yi wa yarinyar fyade. Bayan dukkansu biyu sun aikata danyen aikin ne sai yarinyar ta kasa jure zafin da take ji a gabanta, inda ta fara yin kuka tana ihu, wadda hakan ya jawo hankalina da wasu abokaina da muke wucewa ta ginin a lokacin, inda nan da nan muka yanke shawarar shiga ginin don ganewa idanunmu abin dake faruwa.
“Muna shiga sai muka ga wadanda ake zargin suna kokarin lallabar yarinyar don tayi shuru, da hakan yasa muka fahimci abin da ke faruwa a wajen, sannan muka kama su muka kuma sanar da ‘yan unguwan kafin daga bisani aka garzaya da su tare da yarinyar zuwa ofishin Hukumar tsaron farin kaya ta Cibil Defence dake kusa da mu,” Inji Mustapha.
Daga nan ne sai wakilinmu ya tuntubi mai magana da yahun hukumar ta Cibil Defence a babban ofishinsu dake Lafiya, Kenedy Mathew don jin ta bakinsa dangane da lamarin, inda ya tabbatar da aukuwarsa ya kuma bayyana cewa bayan wadannan matasa da suka kamo wadanda ake zargin sun kawo su wurin jami’ansa suka tsare su. A halin yanzu kuma a cewarsa suna gudanar da cikakken bincike akan lamarin dangane da abin da suka aikata, sannan ya ce da zaran sun kammala binciken za su tura wa ‘yan sanda su kara nasu binciken, sannan a gurfanar da su gaban kotu don su fuskanci hukunci a hukumance.
Ita kuma yarinyar a cewarsa a halin yanzu bayan sun gano jini na cigaba da fitowa daga gabanta ba su yi wata-wata ba sun sanar da iyayenta sannan suka garzaya da ita wani asibiti da ya ce ba zai bayyana sunansa ba cikin gaggawa, don samun kulawar gaggawa daga lilitoti, sannan su kuma bincika ko ta kamu da wata cuta daga wadanda ake zargin.
Haka kuma ya yi amfani da damar inda ya gargadi matasa da sauran masu aikata ire-iren laifukan da su yi hattara, su sauya tunaninsu don a cewarsa a shirye hukumar take ta ci gaba da hada hannu da sauran jami’an tsaro a jihar da al’ummar jihar baki daya wajen bankado tare da hukunta duk wanda aka kama da laifi kowane iri ne a fadin jihar.