Magidanta: Ku bi Umarnin Allah Game Da Iyalinku (2)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban tunatarwa ga magidanta wajen tsare amanar da Allah Ya ba su game da iyalinsu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.3. Yin Kyakkyawar Musaya Don ’Ya’yanka: Kowane uba yana son ’ya’yansa su rika […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban tunatarwa ga magidanta wajen tsare amanar da Allah Ya ba su game da iyalinsu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
3. Yin Kyakkyawar Musaya Don ’Ya’yanka: Kowane uba yana son ’ya’yansa su rika kaunarsa sosai, su rika yawan kewarsa idan baya nan; kuma bayan ya kaura daga duniya su rika yawan yi masa addu’a da yin kyawawan ayyuka dominsa; tabbas duk wanda ya samu haka ya dace da babbar falala abin alfahari a duniya kuma dalilin tsira a lahira in Allah Ya so.
Ba mahaifin da zai dace da haka sai wanda ya sadaukar da lokacinsa, karfinsa da guzarinsa ga ’ya’yansa, wannan ne kadai zai haifar da shakuwa mai cakude da kauna tsakaninsa da su, irin wannan shakuwar ce ke sa yawan bege da kewa da jin dadin rai.
In muka yi dubi ga yadda ci gaban zamani ya dagula yanayin zamatakewar iyali da kuma irin yanayin mu’amular da da mahaifi take a kasar Hausa; hakan ya sa mahaifa maza da dama ba su samun isasshen lokacin da za su sadaukar wajen kulla shakuwa tsakaninsa da ’ya’yansu. Ramadan wata dama ce ga magidantan da ke fama da karancin shakuwa da ’ya’yansa na su yi tsiron sabuwar shukar kyakkyawar dangantaka wacce za ta yi ta girma har karshe.
Sinadarin Rayuwa shi ne abin da magidanta za su sadaukar don yin sabon tsiron kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da ’ya’yansu. Lokaci shi ne sinadarin rayuwar dan Adam domin shi ne, abin da ya fi komai muhimmanci a rayuwa gaba daya.
Sai dai zamani ya sa wasu iyayen sun yi musayar wannan nagartaccen sinadari da kayan alatu da more rayuwar duniya; ta yadda suke kai matuka wajen sama wa ’ya’yansu dukkan kayan bukatun rayuwa, amma su kasa ba su mafi girman kyauta, watau lokaci.
Kasancewar watan Ramadan mafi tsadar lokaci a cikin lokuta duka, sai magidanta su yi amfani da shi wajen sadaukar da sinadarin rayuwasu ga ’ya’yansu ta wadannan hanyoyin:
• Basu Tarbiyya: Gurbacewar zamani ta fara yin nisa ta yadda iyaye kadan ke kula da tarbiyyar ’ya‘yansu; don haka ya kai magidanci, ka yi kokari ka zama daga cikin ’yan kadan din nan masu kula da tarbiyyar amanar da Allah Ya damka a hannunsu; kuma kada ka yadda ka zama daga cikin wadancan masu yawan da za su sha wahala ranar hisabi, saboda kasawar su ga kula da tarbiyyar ’ya’yansu. Lallai babu wani abu mafi muhimmacin da iyaye za su ba ’yayansu da ya wuce kyakkyawar tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci Madaukaki; domin tarbiyya mai kyau ta isa kowane yaro samun rayuwa mai kyawu, kuma abin yabo a duniya da lahira.
Kada ka bari ’ya’yanka su zama fitina a gare ka, ka zama solobiyon uba, ka bar su a sake kamar tumaki babu tarbiyya; burinka ka jiyar da su dadi, ka hore masu duk abin da suke so, can gaba rayuwarsu ta dagule a duniya kuma a lahira su sha wahala wajen hisabi. Komin wuya komin runtsi, ka dage ka baiwa diyanka kyakykyawar tarbiyya; koda yanzu suna ganin ka takurasu da yawa can gaba zasu ji dadi kuma zasu fahimci cewa lallai kaunarka garesu ta cika shiyasa ka dage ga basu tarbiyya. Tarbiyya bata samu sai an sadaukar da lokaci ta hanyar zama tare da su, sa ido da nazarin halin da kowannensu ke ciki, yawan yin hira da su don a fahimci yanayin halayya da tunaninsu, da haka har za a gano wani hali ko tunani marar kyawu a yi kokarin canza shi.
• Koyar Da su Addini: Yana da kyawu uba ya tanadi wani lokaci don koyar da addini ga ’ya’yansa, ya binciki ilmin addininsu, karfin tauhidinsu da kuma yanayin ibadunsu; duk inda ya ji suna bukatar gyara ko karin bayani sai ya yi musu. Ya koya musu son Annabi SAW da ahlin gidansa da Sahabbansa RA. Ya koya musu jajircewa da cijewa wajen bin dokokin addini sau da kafa, ya koya musu karfin hali da danne zuciyarsu daga soye-soyenta. Da sauran kyawawan dabi’un da za su amfane su duniya da lahira.
• Shirya abubuwan ibada tare da su: watan Ramadan watan ibada ne, don kara kusanci da zakin shakuwa da ’ya’yanka, sai ka shirya hanyoyin da za ku kusanci Allah tare da su. Ana iya yin haka ta hanyar zuwa masallaci tare da su ko da yaushe; da yin Sallar Tarawiy cikin Jam’i tare da ’ya’yanka; in ka yi musu limanci yau, gobe ka ba wani daga cikinsu dama ya yi, jibi wani. Haka ma kiran sallah sai a raba shi tsakaninsu. Sai yin Musaffar karatun kur’ani tare da su, suna karantawa kana lura da inda gyara yake kana kokarin gyara musu. daukarsu zuwa sauraren tafsir a Masallaci da sauransu kyawawan ayyuka.
• Nishadantar Da su: Kada uba ya bar mutanen da ake nunawa a talabijin, tatsunniyoyin zamani marasa ma’ana su zama su ne abubuwan nishadantarwa ga ’ya’yansa; lallai yin hakan babban kuskure ne; don haka sai uba ya yi musayar haka da sadaukar da lokacinsa wajen nishadantar da ’ya’yansa da kansa; yin haka zai dace da alheri uku: ladar kyautatawa; kulla shakuwa da kyakkyawar dangantaka da iyalinsa; ga kuma dadin da yin hakan zai haifar a cikin zuciyarsa da na ’ya’yan nasa, wanda haka zai saukar da aminci da kwanciyar hankali cikin iyalinsa. Uba na iya nishadantar da ’ya’yansa cikin wannan wata ta hanyar yin abubuwan nishadi da su bayan sahur ko bayan buda baki. Misali, bayan an gama sahur don hana su koma wa barci kafin yin sallar asuba, sai uba ya yi musu kacici-kacici, tare da tanadar wata ’yar kyauta mai kayatarwa, duk wanda ya canki daidai sai a ba shi. Bayan buda baki kuma, kafin sallar Isha’i uba na iya yin wasan Odiyo-diyo ’ya’yansa ko da na minti biyar ne kadai, wannan zai wartsakar da su da karin masu kuzari har ba za su ji nauyi yin Sallar Tarawiy ba.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.