Magidanta uku na taƙaddama kan mallakar ’ya’yan wata mata a Oyo 

Kowanne na jayayyar cewa shi ne mijin matar da ta haife su na haƙiƙa.

Magidanta uku na taƙaddama kan mallakar ’ya’yan wata mata a Oyo 

Wasu magidanta uku a birnin Ibadan na Jihar Oyo na taƙaddama da juna a kan mallakar wasu ’ya’ya biyu, inda kowanne yake ikirarin shi ne mahaifinsu.

Magidantan uku — Sharafa da Oseni da Rauf — kowanne na jayayyar cewa shi ne mijin matar da ta haife su na haƙiƙa.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi mukabala a tsakanin mazan uku a cikin wani shiri da gidan Rediyon Agidigbo 88.7 FM da ke Ibadan ya gabatar wa masu sauraro.

A cikin mukabalar, an jiyo muryar duk waɗannan mutanen uku kowanne yana cewa ya amince da auren matar mai suna Taiba Raman.

Kowanne daga cikin mutanen uku na ikirarin cewa sun auri matar ce bayan kulla yarjejeniya da ita bisa sharaɗin biyan bashin kuɗin da ake bin wata ’yarta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, kowanne daga cikin mazajen ya amince cewa ya biya wannan kuɗi kafin a kai ga ɗaura auren tsakaninsa da matar.

Cikin bayanin da ta yi wa masu sauraro, Taiba Raman ta tabbatar da cewa duka mutane ukun sun biya bashin kuɗin da ake bin ’yarta kuma duk ta yarda cewa ta auri kowannensu ta riƙa saduwa da su a lokaci ɗaya.

Sai dai ta ce ɗaya daga cikin su mai suna Rauf shi ne uban ’ya’yan biyu na haƙiƙa.

Aminiya ta ce har zuwa lokacin da aka kammala mukabalar, ba a iya tabbatar da mutum ɗaya a matsayin mahaifin ’ya’yan biyu ba, inda kowanne ya dage cewa shi ne ubansu.

Yanzu haka an fara shirin miƙa wannan dambarwa ga jami’an tsaro da ake sa ran bayan sun yi wa waɗannan mutane tambayoyi za su tura su yin gwajib ini a Asibiti domin gano ainihin uban ’ya’yan na haƙiƙa.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa