Magidanta za su fara hutun haihuwa a Legas
Magidantan da ke aikin gwamnatin a Jihar Legas, sun bayyana jin dadinsu dangane da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ba su hutun kwanaki 10 ga wadanda matansu suka haihu.Hakazalika ma’aikata mata ma sun yaba wa gwamnatin jihar kan kara hutunsu na haihuwa daga watanni uku zuwa watanni shida.Wani ma’aikaci da Aminiya tattauna da […]
Magidantan da ke aikin gwamnatin a Jihar Legas, sun bayyana jin dadinsu dangane da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ba su hutun kwanaki 10 ga wadanda matansu suka haihu.
Hakazalika ma’aikata mata ma sun yaba wa gwamnatin jihar kan kara hutunsu na haihuwa daga watanni uku zuwa watanni shida.
Wani ma’aikaci da Aminiya tattauna da shi mai suna Bamidele Kayode ya bayyana cewa yin hakan zai sanya ma’aikata maza su daina guna-gunin bambancin da ake nuna musu kan hutun haihuwa.
‘Gaskiya mun ji dadi kwarai da gaske. Mun dade muna neman wannan abu ga shi Allah ya cika mana burinmu. Mun dade muna gunagunin ana nuna mana bambanci. Ta yaya za a ce idan mace ta haihu an ba ta hutu, amma shi maigidan ba za a ba shi hutu ba? Ai ba ita kadai take daukar dawainiyar yaron ba, shi ma uba yana taka tasa rawar’. In ji shi.
Shi ma Ayo Papoola ya ce ‘Na ji dadi kwarai da gaske da na samu labarin gwamnati za ta rika ba mu hutun kwanakin 10. Domin zai taimaka kwarai da gaske, kuma zai rage bambancin da ake da shi tsakanin maza da mata a harkar aikin gwamnati. Sai dai ina kira ga gwamnati ta kara mana kwanaki don mu ma mu samu damar duba iyalanmu’.
Misis Iyabo Adekunle cewa ta yi ‘Mun yi murna da gwamnati ta kara mana hutun haihuwa daga watanni uku zuwa watanni shida. Hakan zai ba mu damar mu yi raino cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya, kuma yaranmu za su samu lafiya kwarai da gaske’.
Gwamnatin Jihar Legas ta bullo da hutun kwanaki 10 ga magidantan da matansu suka haihu, sannan ta kara hutun ma’aikata matan da suka haihu daga watanni uku zuwa watanni shida.
Shugabar ma’aikatan jihar, Misis Josephine Williams ta ce gwamnati ta bullo da hutun ne don ta rage radadin aiki ga iyaye.
Ta ce ‘Ma’aikaciya mace za a ba ta hutun makonni 24 yayin da ta haihu tare da biyanta albashinta cikakke a haihuwarta ta farko da ta biyu. Za ta fara hutun makonni biyu kafin ranar haihuwarta, sannan shi ma’aikacin da aka yi wa haihuwar yana da hutun kwanaki goma’.
Ta kara da cewa ‘Amma sauran hayayyafar da macen za ta yi daga baya za a ba ta hutun makonni 12 ne kawai, shi kuwa namijin ba zai samu hutun kwanaki 10 ba’.