Magoya bayan APC a Kuros Riba sun nemi a tsige shugabansu
Tun bayan kammala zaben Shugaban kasa da na gwamnoni a Jihar Kuros Riba, inda jam’iyyar APC ba ta samu koda dan majalisar dokoki ba bare ma ta wakilai ko dattawa, lamarin da yanzu haka ya jawo zargin juna matuka tsakanin shugabannin jam’iyyar da magoya bayansu, wadanda suka bukaci nan take ba tare da wani jinkiri […]
Tun bayan kammala zaben Shugaban kasa da na gwamnoni a Jihar Kuros Riba, inda jam’iyyar APC ba ta samu koda dan majalisar dokoki ba bare ma ta wakilai ko dattawa, lamarin da yanzu haka ya jawo zargin juna matuka tsakanin shugabannin jam’iyyar da magoya bayansu, wadanda suka bukaci nan take ba tare da wani jinkiri ba jam’iyyar APC matakina kasa ta cire Usani Usani daga mukaminsa na shugaban jam’iyya a jihar, sakamakon zarginsa da ake yi da yi wa jam’iyyar makarkashiya, sannan kuma zargin sa da karkata Naira milyan 100, da uwar jamiyyar ta kasa ta ware domin a raba wa ’yan takara su yi yakin neman zabe tun daga matakin Shugaban kasa da na gwamna zuwa na majalisar jihohi.
Wakilinmu da ya halarci taron da jam’iyyar ta gabatar, wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, shugabannin jam’iyyya matakin unguwanni da mazabu, sun bayyana shakkunsu cewa, yaya za a yi duk da irin kudin da aka ware, domin ba ’yan takara a nemi jama’a, a ce APC ko kujerar dan majalisa daya ba ta samu ba? A nan ne wani daga cikin shugabannin jam’iyyyar matakin gunduma daga mazabar Ikom ya mike ya ce: “Magana ta gaskiya mun ci amanar APC, domin wasu daga ciki mu sun zabi PDP wasu kuma APC a zaben Shugaban kasa, yayin da wasu kuma da aka zo zaben gwamna ’yan jam’iyyyar APC, maimakon su zabi dan takarar APC sai wasu suka zabi na LP, wasu kuma APC, yayin da wasunmu kuma na PDP. Don haka ba abun mamaki ba ne don haka ta faru.” Bayan jin wancan jawabai sai hayaniya ta kaure a zauren taro har ma aka kusa ba hammata iska amma dai an yi kumfar baki. Da kura ta lafa, masu jawabi na gaba kuma kira suka yi da cewa lallai ba su ga amfanin shugaban jam’iyyar APC na Kuros Riba ba, Usani Usani. Daga nan suka bukaci a tsige masu shi
Aminiya ta tuntubi wanda ake zargi, Usani Usani, shugaban jam’iyyar ta waya, ya ce: “Ba na gari, wannan ba batu ne da za a yi maganarsa ta waya ba, sai na dawo daga Abuja zan waiwayi Aminiya.”