Magoya bayan Buhari sun shirya tattaki a Abuja

Kungiyar magoya bayan Shugaba Buhari (I stand With Buhari) ta shirya gudanar da tattaki a ranar Laraba a Abuja. Kungiyar ta ce tuni ta sanar da shugaban ‘yan sanda game da tattalin nata wanda ta ce tana sa ran zai ta tara mutum miliyan goma, domin nuna cikakkiyar goyon bayansu ga Buhari. Buhari ya gana […]

Magoya bayan Buhari sun shirya tattaki a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Kungiyar magoya bayan Shugaba Buhari (I stand With Buhari) ta shirya gudanar da tattaki a ranar Laraba a Abuja.

Kungiyar ta ce tuni ta sanar da shugaban ‘yan sanda game da tattalin nata wanda ta ce tana sa ran zai ta tara mutum miliyan goma, domin nuna cikakkiyar goyon bayansu ga Buhari.

Shugaban kungiyar, Ogochukwu Ezeaku ya ce za su fara tattakin ne daga Unity Fountain da ke unguwar Maitama.

An tambaye shi ko ya yake ganin za ta kaya tsakaninsu da masu zanga-zangar #EndSARS, sai ya ce ya san masu zanga-zangar ba su masu tayar da rikici ba ne.

Ya ce manufar tattakin ita ce nuna wa duniya yawan magoya bayan Buhari har gobe.