…Magoya bayan Chile sun kai wa iyalan Lionel Messi hari
A ranar Asabar da ta wuce ne aka samu labarin wadansu magoya bayan Chile sun kai wa iyalan Lionel Messi hari a lokacin da ake wasan karshe a tsakanin Chile da Ajantina a gasar cin kofin Copa Amerika. Kafar watsa labaran wasanni ta Goal.com ta kalato cewa wasu daga cikin magoya bayan Chile ne rika […]
A ranar Asabar da ta wuce ne aka samu labarin wadansu magoya bayan Chile sun kai wa iyalan Lionel Messi hari a lokacin da ake wasan karshe a tsakanin Chile da Ajantina a gasar cin kofin Copa Amerika.
Kafar watsa labaran wasanni ta Goal.com ta kalato cewa wasu daga cikin magoya bayan Chile ne rika zagin iyalan Messi ta uwa-ta-uba a bangaren ’yan kallo a lokacin da wasa ke gudana. Hakan ce ta sa dan uwan Messi mai suna Rodrigo, dan kimanin shekara 28 ya rika rama zagin da ake musu, al’amarin da ya harzuka masu zagin nasa kuma suka shiga jibgarsa. Sai da jami’an tsaro suka shiga tsakani inda suka tserar da su a dakin talabijin da ke watsa yadda wasan ke gudana kafin magoya bayan su hakura.
Shi ma iyalan dan kwallon gaba a Ajantina Sergio Aguero ba su tsira ba, don magoya bayan Chile sun muzanta su a bangaren ’yan kallo a lokacin da wasan ke gudana.
Shi kuma Lionel Messi an yi ta yi masa keta a lokacin wasan al’amarin da ya sa bai sha ta da dadi ba ga shi kuma kasarsa ta rasa kofin.