Magoya bayan Jam’iyyar APC dubu uku sun canja sheka zuwa PDP a Gombe

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu magoya bayan Jam’iyyar APC suka canja sheka daga jam’iyyar zuwa PDP a karamar Hukumar Yamaltu Deba da ke Jihar Gombe.Da yake karbar wadanda suka canja shekar a filin wasa na garin Deba, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Mista Shu’aibu Baba Sabulu, kira ya yi da kada […]

Magoya bayan Jam’iyyar APC dubu uku sun canja sheka zuwa PDP a Gombe
Magoya bayan Jam’iyyar APC dubu uku sun canja sheka zuwa PDP a Gombe

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu magoya bayan Jam’iyyar APC suka canja sheka daga jam’iyyar zuwa PDP a karamar Hukumar Yamaltu Deba da ke Jihar Gombe.
Da yake karbar wadanda suka canja shekar a filin wasa na garin Deba, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Mista Shu’aibu Baba Sabulu, kira ya yi da kada a nunawa wadanda suka canja shekar bambanci.
Mista Baba Sabulu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Nasiru Aliyu Gwani, ya ce tunda sun canja sheka za a karbe katunansu na APC a ba su sababbi na Jam’iyyar PDP. Kuma ya ce duk wani taro da za a gudanar na PDP da su za a rika yi.
A jawabin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe Alhaji Inuwa Garba, ya ce mutanen sun koma PDP ne domin kishin karamar hukumarsu da Jihar Gombe.
Alhaji Inuwa Garba, ya ce yanzu karamar Hukumar Yamaltu Deba babu sauran ’yan adawa domin duk mai kishin ci gaban jihar dan asalin karamar hukumar ya bar adawa ya zo ya yabi don haka sai ya kirayi ’ya’yan jam’iyyarsu ta PDP su rungumi juna a tafi tare don a samu kaiwa gaci.
Adamu Aliyu Adamu na cikin wadanda suka canja shekar, ya shaida wa wakilinmu cewa ra’ayinsa ne ya sa ya bar APC ya koma PDP, amma an ba shi Naira dubu daya ya kuma karba saboda kudin jam’iyya ne.
Shi ma Muhammad Umar, wanda ya ce ya koma PDP ne saboda ya ga mutane masu yawa daga yankin nasu sun koma.
Wadanda suka canja shekar dai sun kai mutum 3,340 kuma manyan ’ya’yan yankin taron da suka hada da shugaban majalisar jihar da kwamishinoni da masu taimaka wa Gwamna ne suka halarta.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi