Magoya bayan Man United sun ci mutuncin Pogba
Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Manchester United da ke Ingila sun nuna cewa wadansu magoya bayan kulob din sun shiga kafar sada zumunta ta Twitter suka ci mutuncin Paul Pogba ta hanyar yi masa bakaken maganganu musamman a matsayinsa na bakar fata bayan ya barar da bugun finareti a wasan da kulob din […]
Paul Pogba
Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Manchester United da ke Ingila sun nuna cewa wadansu magoya bayan kulob din sun shiga kafar sada zumunta ta Twitter suka ci mutuncin Paul Pogba ta hanyar yi masa bakaken maganganu musamman a matsayinsa na bakar fata bayan ya barar da bugun finareti a wasan da kulob din ya yi kunnen doki da ci 1-1 da na Wolbes a ranar Litinin da ta wuce.
Manchester United ta yi wasanta na biyu ne da kulob din Wolbes a ranar Litinin inda aka tashi wasan ne da ci 1-1.
Sai dai a yayin wasan United ta samu bugun finareti kuma Paul Pogba ne ya buga bayan sun yi sa-in-sa da Marcus Rashford. Jim kadan bayan Pogba ya buga finaretin ne sai ya barar kuma hakan ya sa da yawa daga cikin magoya bayan kulob din sakamakon wasan bai yi musu dadi ba.
Magoya bayan da suka rika zagin Pogba a shafin Twitter sun yi haka ne don huce haushinsu kan yadda dan kwallon ya zubar da damar da suka samu ta doke kulob din Wolbes a wasan amma suka kare da yin kunnen doki.
Sai dai akwai yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ya Ingila (FA) ta hukunta magoya bayan da suka yi haka, don al’amari ne da ya saba wa dokar kwallon kafa a duniya musamman zagi ko cin mutunci ko nuna wariyar launin fata ga wani dan kwallo.