Magoya bayan Manchester United za su yi zanga-zanga a Old Trafford

Za mu farfaɗo kuma kakar wasa ta bana za ta yi mana kyau a cewar Ten Hag.

Magoya bayan Manchester United za su yi zanga-zanga a Old Trafford

Filin wasa na Old Trafford na Manchester United

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za su yi zanga-zanga ranar Asabar a filin wasa na Old Trafford.

Zanga-zangar za ta gudana ne a matsayin wani mataki na nuna adawa ga mamallakan kulob ɗin kafin wasan United da Luton inda suke buƙatar a sayar da ƙungiyar.

Ƙungiyar magoya bayan United ta dakatar da adawa da dangin Glazer bayan mutuwar Sir Bobby Charlton, daya daga cikin fitattun ’yan wasa da suka haska a kungiyar.

Magoya bayan na bukatar ganin an kammala sayar da kungiyar ce domin bai wa masu sha’awar zuba jari karbar ta da kuma zuba makudan kudade don tada komadarta da zummar ganin ta dawo da karsashin da aka santa da shi na gogayya a tsakaninta da manyan kungiyoyin da ke Turai.

Sai dai sun yi kira ga magoya bayansu da su hallara a kusurwar Arewa maso Yammacin filin wasan domin abin da suka bayyana a matsayin zanga-zangar lumana.

Wannan dai za ta kasance zanga-zanga ta farko tun bayan da aka bayyana cewa Sir Jim Ratcliffe na fatan sayen ƙaramin hannun jari a kulob ɗin, a wani mataki da ke nuna cewa dangin Glazer za su ci gaba da kasancewa masu rinjaye.

Bugu da ƙari, ana sa ran Ratcliffe zai sanya kusan fam miliyan 245 na kuɗinsa don yin aikin garambawul a filin wasan.

Majiyoyi da dama daga ciki da wajen United sun shaida wa BBC cewa dole ne a hanzarta gaggawar sauya ikon mallakar ƙungiyar, wanda aka ƙaddamar kusan watanni 12 da suka wuce, saboda rashin tabbas da ake fama da shi ba ya taimaka wa kociyan ƙungiyar Erik ten Hag.

United ta yi rashin nasara a wasa na tara cikin 17 a kakar wasan bana kuma tana fuskantar yiwuwar gaza kai wa zagaye na gaba a Gasar Zakarun Turai.

Sau huɗu ne kawai suka kai zagaye na biyu a gasar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya daga aikin horas da ’yan wasa a shekarar 2013.

Za mu farfaɗo — Ten Hag

Shi kuwa kociyan kungiyar, Erik ten Hag ya ce ya shaida wa ’yan wasansa cewa kakar wasan bana “za ta yi mana kyau.”

A yanzu dai United tana matsayi na ƙarshe a rukuninta na Gasar Zakarun Turai bayan ta sha kashi a hannun FC Copenhagen kuma tana matsayi na takwas a teburin Firimiyar Ingila.

Dukan da United ta sha a hannun Copenhagen da ci 4-3 ya janyo ce-ce-ku-ce, musamman saboda jan kati da aka nuna wa Marcus Rashford lokacin da Red Devils ke ci 2-0.

Rashford ya taka ƙafar Elias Jelert, lamarin da ya sa aka tura alƙalin wasa Donatas Rumsas zuwa wajen duba alƙalin wasa na bidiyo da ke gefen filin wasa, kuma daga nan ya bai wa Rashford jan kati.

“Na ji takaici matuka game da irin wannan hukunci, ina ganin bai kamata a ce wasan ya kasance haka ba,” in ji Ten Hag.

Ya kuma ƙara da cewa “Za mu ci gaba da gwagwarmaya saboda ina da tabbacin cewa sa’ar mu za ta sauya—a lokaci guda a kakar wasan nan za ta yi mana kyau.”

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda