Magoya bayan Nasarawa United sun zabi sababbin shugabanni
kungiyar Magoya Bayan Kulob din Nasarawa United na Jihar Nasarawa ta zabi sabon shugabanta. A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Lafiya, kungiyar ta bayyana Abdullahi Abubakar a matsayin sabon shugaban kungiyar sai Abubakar Ibrahim a matsayin mataimakin shugabasai Bala Muhammed Galadima a matsayin Ma’aji. Usman Mohammed Aliyu ne aka zaba a […]
kungiyar Magoya Bayan Kulob din Nasarawa United na Jihar Nasarawa ta zabi sabon shugabanta. A wata sanarwa da aka raba wa manema
labarai a Lafiya, kungiyar ta bayyana Abdullahi Abubakar a matsayin sabon shugaban kungiyar sai Abubakar Ibrahim a matsayin mataimakin shugaba
sai Bala Muhammed Galadima a matsayin Ma’aji. Usman Mohammed Aliyu ne aka zaba a matsayin sakatare sai Haruna Dogara Mainingi shine a matsayin sakataren kudi. Haka kuma an zabi Alhassan Musa Shariff a matsayin mai magana da yawun kungiyar.
A jawabinsa jim kadan bayan an zabi sababbin shugabannin kungiyar, shugaban marubuta labarin wasanni a jihar, danmusa Mohammed ya yaba wa kungiyar magoya bayan kulob din Nasarawa United dangane da zabo sababbin shugabannin da suka yi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba inda ya yi alkawarin hada hannu da sababbin shugabannin don daukaka martabar kungiyar zuwa matsayi na gaba. Daganan sai ya yi kira ga ‘ya’yan kungiyar su ba wa sababbin shugabanninsu cikakken goyon baya don su cimma nasara.
Shi dai sabon shugaban kungiyar magoya bayan kulob din Nasarawa United, Abdullahi Abubakar ya tsaya takarar kujerar ce da takwaransa Alhaji Muhammed Sakkwato amma ya janye masa.