Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano
Mutanen dai na neman kotun daukaka kara ta yi wa Abba adalci
Wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP sun fantsama a kan titunan birnin Kano suna zanga-zangar neman kotun daukaka kara ta yi wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, adalci.
Mutanen dai sun yi zanga-zangar ce da yammacin Laraba don su nuna bacin ransu kan ce-ce-ku-cen da suka ce hukuncin kotun na ranar Juma’a ya janyo sakamakon tufka da warwarar da suka ce yana cike da shi.
- Kano: Kundin shari’ar Kotun Daukaka Kara ya tabbatar da nasarar Abba —Dederi
- Gobara ta tashi a Hukumar Shari’ar Jihar Kano
Mutanen dai sun halarci wata sallah ta musamman ne a filin Mahaha da ke Ƙofar Na’isa a birnin na Kano wajen misalin ƙarfe 2:00, daga bisani sun fantsama tituna suna neman a yi wa jam’iyyarsu da ɗan takararta adalci.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan bayyanar kundin hukuncin kotun na ainihi da a wasu shafukansa ya nuna kotun ta jingine hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben da ya dakatar da Abba sannan ya ayyana Nasir Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ga wasu daga cikin hotunan zanga-zangar: