Magoya bayan Pillars za su cigaba da karfafa wa ’yan kwallonsu gwiwa

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za su ci gaba da karfafa gwiwar ‘yan wasan su ta yadda kungiyar za ta cimma nasarar lashe gasar firimiya ta bana.  kungiyar ta tabbatarwa da ‘yan wasan cewa  magoya bayan kungiyar za su bi su duk inda suke yin wasa domin ba su karfin zuciyar buga […]

Magoya bayan Pillars za su cigaba da karfafa wa ’yan kwallonsu gwiwa
Magoya bayan Pillars za su cigaba da karfafa wa ’yan kwallonsu gwiwa

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za su ci gaba da karfafa gwiwar ‘yan wasan su ta yadda kungiyar za ta cimma nasarar lashe gasar firimiya ta bana.  kungiyar ta tabbatarwa da ‘yan wasan cewa  magoya bayan kungiyar za su bi su duk inda suke yin wasa domin ba su karfin zuciyar buga wasa  walau a gida ne ko kuma waje.
Wannan albishir  ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars , Alhaji Bashir Mu’azu Jide a zantawarsa da Aminiya, bayan  kungiyar Kano Pillars ta doke kulob din Ifeanyi Ubah a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata a ranar Lahadin data gabata.
Shugaban ya jinjina wa ’yan wasan kasancewa sun fara gasar firimiya ta bana da kafar dama, inda ya hore su da su cigaba da nuna kwazo don ganin sun sake lashe gasar a karshen kakar wasa ta bana.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa