Magoya bayan Trump sun lashi takobin kare shi a batun tsige shi

Yayin da ake tsammani Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri’ar tsige Shugaba Donald Trump a wannan mako, fadar White House ta maida hankalinta ne kan Majalisar Dattawan kasar da ’yan Jam’iyyar Republican ke da rinjaye, inda Shugaban Kasar zai fuskanci tuhuma a farkon watan Janairu. Shugaba Trump da mukarrabansa suna shirin ci gaba da […]

Magoya bayan Trump sun lashi takobin kare shi a batun tsige shi

Yayin da ake tsammani Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri’ar tsige Shugaba Donald Trump a wannan mako, fadar White House ta maida hankalinta ne kan Majalisar Dattawan kasar da ’yan Jam’iyyar Republican ke da rinjaye, inda Shugaban Kasar zai fuskanci tuhuma a farkon watan Janairu.

Shugaba Trump da mukarrabansa suna shirin ci gaba da kare shi cikin hanzari kuma ta kowace hanya, tare da burin juya al’amari kan ’yan adawa na Jam’iyyar Democrat.

A wannan mako, ’yan Jam’iyyar Democrat da ke da rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka ake tsammani za su kada kuri’ar tsige Shugaba Donald Trump a kan tuhume-tuhumen yin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma hana ’yan majalisa gudanar da aikinsu.

Shugaba Trump zai fuskanci tuhuma a Majalisar Dattawan Amurka, inda ’yan Democrat suke so su ji daga karin wasu shaidu, cikinsu har da Mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House, Mick Mulbaney da tsohon mai bada shawara kan tsaron kasa, John Bolton.

Yanzu da binciken yake komawa zuwa ’yan Republican da ke da rinjaye a Majalsiar Dattawa, Fadar White House ta canja dabarunta gaba daya. Suna aiki yanzu haka da jagororin ’yan Republican don a yi sauri a kammala binciken kana a rage irin barnar da zai yi a siyasance.