Magoyan bayan NNPP sun yi murnar nasarar Abba Gida-Gida a Kuros Riba

Nasarar da Abba ya samu a shari’ar ta buɗe wani sabon babi na yafiya a siyasar Kano da kasa baki daya.

Magoyan bayan NNPP sun yi murnar nasarar Abba Gida-Gida a Kuros Riba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP da ke zaune a Unguwar Hausawa ta Jihar Kuros Riba, sun yi murnar nasarar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Koli.

A Juma’ar da ta gabata ce dai Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayi halastaccen Gwamnan Kano bayan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara sun haramta masa kujerar.

Dalilin haka ne magoya bayan jam’iyyar NNPP a Kalaba, babban birnin Kuros Riba, suka hau tituna suna bayyana farin cikinsu tare da raba wa juna kayan tanɗe-tanɗe da maƙwalashe.

Wakilinmu ya ruwaito Alhaji Danjuma Mohammed, Shugaban jam’iyyar NNPP bangaren ’yan Arewa yana cewa, nasarar da Abba Gida-Gida ya samu a shari’ar ta buɗe wani sabon babi na yafiya a siyasar Kano da kasa baki daya.

“Kotu ta yi adalci a wajen yanke humuncin sannan ina kira ga ’yan adawa da su zo a tafi tare domin yi wa jiha aiki da kuma ciyar da ita gaba.”

Ya ci gaba da cewa “Hakika Kotu ta yi adalci wajen gudanar da aikinta domin kafin yanzu har wasu daga cikin ’yan kasa sun fara dawowa daga rakiyar kotunan suna zargin ko sun fara zama ’yan amshin Shata,” inji shi.

Haka kuma, ya shawarci Kanawa da su mara wa Gwamnan baya wajen yi wa jama’a aiki, yana mai tunatar da Gwamnan ya mayar da hankali wajen inganta harkokin ilmi da kiwon lafiya musamman idan an yi la’akari da yadda wasu asibitoci da makarantu suka lalace.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa