Magudanar ruwa ta ci mutum biyu a Legas
Wasu mutum biyu sun mutu, daya ya karye, yayin da suka fada wata magudanar ruwa da ke unguwar Afanla a cikin karamar Hukumar Agege da ke Legas.A kwanakin baya, magudanar ruwan ta ci ran mutane da dama, kuma wasu jama’a masu yawa suka samu raunuka.daya daga cikin iyayen unguwar Afanla, Alhaji Ramadan Musa danjalo ne […]

Wasu mutum biyu sun mutu, daya ya karye, yayin da suka fada wata magudanar ruwa da ke unguwar Afanla a cikin karamar Hukumar Agege da ke Legas.
A kwanakin baya, magudanar ruwan ta ci ran mutane da dama, kuma wasu jama’a masu yawa suka samu raunuka.
daya daga cikin iyayen unguwar Afanla, Alhaji Ramadan Musa danjalo ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata. “Gaskiya wannan kwalbati, idan har gwamnati ba ta gyara ta ba, muna iya cewa ta ci amanar mu, domin mutane suna fadawa ciki suna mutuwa. A kwanan nan ma an sami wani mutum a ciki ya mutu, sannan an sami wata mata da ta fada ciki ta karya kafa. Yau bai fi kwanaki uku ba, aka sami wani mutum ya mutu a ciki. Amma gwamnati ta yi shiru kuma kamfanin da yake aikin sai jan kafa yake yi dangane da batun aikin, ya ki gama aikin cikin lokaci. Ba mu san dalilin da ya sa suke yi mana abin da suka ga dama ba game da kammala aikin a wannan yankin namu, amma wasu yankunan duk an gyara musu magunan ruwansu.
“Wannan kwata ta jawo mana cutar maleriya, saboda kazantar da ake zubawa a wurin, saboda haka ina kira ga bankin duniya da gwamnatin Jihar Legas su dauki matakan da suka dace don ganin an kammala aikin cikin lokaci, domin duk kokarin da muka yi na ganin an kammala aikin cikin lokaci ya ci tura”. Inji shi.
Alhaji danjalo, wanda kuma har ila yau shi ne shugaban kamfanin Kyankyaso Network Links Limited, ya yi tsokacin cewa za su kai kamfanin da ke yin kwangilar aikin a kotu muddin bai kammala aikin ba.
Ya ce idan ba su gaggata kammala aiki nan cikin lokaci ba, “A shirye muke mu shigar da kara kotu domin neman hakkinmu a matsayin mu na ’yan Najeriya da ke da cikakken ’yanci”. Inji shi.
Dangane da katin shaidar dan jiha da gwamnatin Legas ta bullo da shi, danjalo ya shawarci ’yan Arewa da ke zaune a jihar su mallaki katin domin amfanin da yake da shi.