Magujin duniya Ya yi gudun kilomita 580 a Hadaddiyar Daular Larabawa
Wani gwani gudu dan kasar Filifins, mai suna Ceasaer Guarian ya yi guje-guje a kasashen duniya 48, ya karade masarautu bakwai da suka hadu suka yi Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya yi gudun kilomita 580, don neman tallafin Dala miliyan 10 da za a agaza wa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta auka wa a kasarsa […]
Wani gwani gudu dan kasar Filifins, mai suna Ceasaer Guarian ya yi guje-guje a kasashen duniya 48, ya karade masarautu bakwai da suka hadu suka yi Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya yi gudun kilomita 580, don neman tallafin Dala miliyan 10 da za a agaza wa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta auka wa a kasarsa ta Filifins.
Gwanin gudun dai dan shekara 58 ne, ya kuma ce a kowace rana yana shafe kilomita 40 yana gudu: “Wannan gudun da na yi ya fi sauki a kan wanda na yi a kasashen Bahrain da katar da Kuwait da Saudiyya da Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa. Gudun farko ya fi wahala. Kuma a lokacin bazara ne, sannan ina son a lokacin da nike gudu in jike da zufa.”Guarin ya fara gudun ne a ranar 22 ga Nuywambar bana., ya kuma kammala a cikin Disamba. Ya kuma bayyana aniyarsa ta yin gudun a kasashen Amurka ta Arewa, a tsakanin Afrilu da Mayu, sai Japan da Koriya da Sin a tsakanin Satumba zuwa Oktoba. “A kodayaushe ina daukar wannan gudun yankin nahiyoyin duniya, a matsayin sadaukarwa ga daukacin ’yan Filifins. Wannan ita ce hanyar da zan iya nuna musu gamsuwata da sadaukar da kai gare su, musamman wadanda suka bar iyalansu a can. Su suke ba ni kwarin gwiwa,” inji shi.