Magulmata sun so hada ni da Jonathan kan kashe-kashen da ake yi a Arewa – Abdul Ningi

A kwanakin baya ne Sanata Abdul Ahmed Ningi ya nuna bukatarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben badi. Wakilinmu ya tattaunawa da shi game da siyasa da kashe-kashen da ke faruwa a Arewa da abin da ya shafi tattalin arziki da tsaro: Aminiya: Me sanata zai ce ga talakan Arewa a wannan lokaci […]

Magulmata sun so hada ni da Jonathan kan kashe-kashen da ake yi a Arewa – Abdul Ningi
Magulmata sun so hada ni da Jonathan kan kashe-kashen da ake yi a Arewa – Abdul Ningi

A kwanakin baya ne Sanata Abdul Ahmed Ningi ya nuna bukatarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben badi. Wakilinmu ya tattaunawa da shi game da siyasa da kashe-kashen da ke faruwa a Arewa da abin da ya shafi tattalin arziki da tsaro:

Aminiya: Me sanata zai ce ga talakan Arewa a wannan lokaci don ya gamsu ya ba jam’iyyarku ta PDP goyon baya a zabe mai zuwa?
Sanata Ningi:  Da farko ina jajanta mana game da abubuwan da suke faruwa a Arewa musamman Arewa maso Gabas yankin da na fito, saboda wannan al’amari babu wanda bai damu ba musamman mu wakilan jama’a da aka sa a gaba don kare muradun mutanen. Kullum muna nuna takaicinmu da bayyana alhini da rashin gamsuwa kan yadda al’amura ke gudana, hakan ya sa wasu marasa kishi ke cin dunduniyarmu, saboda yadda muke nuna damuwa kan abin da ake yi mana. Tun muna shiru muna hakuri yanz muke fitowa muke nuna wa kowa bacin ranmu a matsayinmu na wakilan mutane. Don haka muna rokon mutane su ci gaba da yyi mana addu’ar Allah Ya isar mana Ya kuma wuce mana gaba Ya tona asirin duk mai mummunar aniya kan Arewa. Kuma duk wani abu da ya yi zafi da yardar Allah zai yi sauki, don haka muke rokon Allah Ya isar mana Ya yi mana maganin masu muguwar manufa ga Arewa.
Aminiya: Me za ka ce kan yadda jam’iyyarku ta PDP ke gudanar da takunta?
Sanata Ningi: A gabanmu aka kafa wannan jam’iyya tun lokacin su Adamu Ciroma, su Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da su marigayi Abubakar Rimi.  Don haka har yanzu muke cikin wannan jam’iyya saboda mun san mutane masu akidar kwarai suka kafa ta, kuma ita ne jam’iyya a hannu yanzu ba ta mutum guda ba ce, ba kuma jam’iyyar Arewa ko Kudu ko ta Musulmi ko Kirista ba ce, jam’iyya ce ta kowa. Kuma ba ma shiga jam’iyya saboda mutum muna shiga ne saboda akida, domin mutum mai mutuwa ne don haka ba na Jam’iyyar PDP saboda Shugaba Jonathan don shi ma a cikinta ya same ni, kuma ba na yin ta saboda Gwamna Isa Yuguda shi ma tare muka shiga. Don haka nake kiran kowane dan PDP kada ya yi wannan jam’iyya saboda Abdul Ningi, ya yi saboda ganin abubuwa suna tafiya daidai. Saboda duk abin da ya taso ana zama a tattauna a tsaya kan tafarkin da mutane ke so. Amma ko gobe aka ce PDP ta zamo jam’iyyar mutum daya, nan take zan fice na koma wata. Don haka idan kansila ake so ko dan majalisa ko duk wani mukami, to a koma wurin mutane su ne masu zabarsu namu taimakawa ne. Ba za mu yi kaka- gida mu tilasta wa mutane dan takara ba, wannan shi ne dadin dimokuradiyya.
Aminiya: Ina aka kwana game da batun tsayawarka takarar Gwamna?
Sanata Ningi: Kamar yadda nake wakiltar mutanen Bauchi ta Tsakiya, haka nake bukatar mutane su ba ni goyon baya na jagoranci wannan jiha, duk wanda ya ce zai raba wannan shiyya ta Bauchi ta Tsakiya domin toshe mu daga yin abin da mutane ke so, dole mu kalubalance shi a kotu. Mutanen wannan shiyya suna da damar yin Gwamna idan jama’a na kaunarsu, kuma a shirye muke ba ma tsoron wani dan siyasa a Jihar Bauchi dole mu kalubalance shi idan ya ce dan Bauchi ta Tsakiya ba zai tsaya takara ba. Muna da hujja muna da martabar neman Gwamna kuma ba za mu ji tsoron kowa ba, wani ya ce dan shiyyar Bauchi ta Tsakiya ba zai yi Gwamna ba wannan mutum na yaudarar kansa ne. A shirye muke mu zaga kowace shiyya a Jihar Bauchi mu nemi goyon bayan mutane mu bayyana musu manufofinmu na ci gaba da muka tanada, tare da jajircewa da za mu yi kan bukatunsu don haka ba za mu yarda da kama- karya ko sakaci da nauyin da Allah Ya dora mana ba, shi ya sa a kullum kuke gani ake rigima da mu wajen kwato hakkin mutanenmu. Tuni na fara taron hada kan jama’a, kuma na shirya tarurruka a garuruwan da suka dace tare da taimaka wa gwargwadon hali a kowace shiyya. Mutanen mazabata suna ganin duk aikin da aka fitar da kudi sai na kawo musu shi har gida kamar yadda doka ta ce, wani ma da kudina nake yi don amfanin jama’ata. Kuma wadannan maganganu da nake yi ba rashin kunya ba ne sanin ’yanci ne, saboda akwai magulmata da suka sani a gaba musamman a lokacin taron da aka yi a Bauchi wasu sun je suna cewa wa Goodluck Jonathan wai ina maganar cewa ana kashe mutanen Arewa ana rufe makarantu, ana lalata mana dukiya, lamarin da ya sa mutanen wannan shiyya ta Arewa maso Gabas suna hijira suna komawa wasu yankuna, to ba gaskiya ba ne? Idan dai wannan magana ce ba za mu daina fada ba, har sai an daina cin zarafinmu, don haka masu fadar wannan magana sun makara, a kan mutanenmu ba ma tsoron kowa, mun yi karatu mun san ’yancinmu ba za mu zubar da martabar mutanenmu da rayukansu a kan abin duniya ba, dole mu fada iyakar karfinmu. Duk wanda ya ce mana kule za mu ce masa cas! Domin dukkanmu ’yan Adam ne ba wanda ya isa ya kashe wani sai kwanansa ya kare, sanin kowa ne duk Najeriya babu kabilar da za a yi mata abin da ake yi wa Arewa a zauna lafiya. Don haka muna rokon jama’a su ci gaba da yi mana addu’a duk kokarin da muke yi kan abubuwan da ke faruwa Allah Ya kare mu Ya kara mana karfin gwiwa. Kuma mutane su ci gaba da Addu’a Allah Ya tona asirin duk masu hannu a cikin kisan gillar da ake yi wa mutanenmu, da fatar Allah Ya kawo mana karshen duk mai hannu cikin wannan bala’i.