Maguna sun fi mutane yawa a tsibirin Aoshima da ke Japan

Maguna sun fi mutane yawa a tsibirin Aoshima da ke Japan. Fiye da maguna 100 ne ke zaune a tsibirin tare da tsofaffi 16, wadanda ke kula da maguna, suna ciyar da su.Tsibirin Aoshima da ke gabar tekun Ozu  kasar Japan, daular  kyanwa ce a duniya, domin maguna sun fi mutane yawa a wannan tsibirin. […]

Maguna sun fi mutane yawa a tsibirin Aoshima da ke Japan
Maguna sun fi mutane yawa a tsibirin Aoshima da ke Japan

Maguna sun fi mutane yawa a tsibirin Aoshima da ke Japan. Fiye da maguna 100 ne ke zaune a tsibirin tare da tsofaffi 16, wadanda ke kula da maguna, suna ciyar da su.
Tsibirin Aoshima da ke gabar tekun Ozu  kasar Japan, daular  kyanwa ce a duniya, domin maguna sun fi mutane yawa a wannan tsibirin. Asali maguna 100.
Asalin zuwan magunan wannan tsibiri, shi ne su kashe beraye da ke shiga cikin jiragen rowan kamun kifi, har ta kai ga sun taru da yawa a wannan wuri. Wadannan maguna sun samu shahara a shafukan intanet tun a shekarar 2015, inda ’yan yawon shakatawa ke zuwa tsibirin na Aoshima don ganin ’yan tsirarun mazaunan wurin tare da dimbin kyanwowi.