Mahafiyar Kachalla Battujo za ta shekara 20 a gidan yari
Kotu ta yanke wa mahifiyar Kachalla Battujo hukuncin ne bayan samun su da laifin taimaka wa ta’addanci ta hanyar taimaka masa da bayanai
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara 20 ga mahaifyar jagoran ’yan bindiga, Kachalla Ibrahim Battujo, wanda sojoji suka kashe shi a makon jiya.
Kafin jami’an tsaro su kashe Battujo, yana daga cikin manyan jagororin ’yan bindiga da suka addabi yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa Safiya Salihu, mahifiyar Kachalla Battujo, hukuncin ne bayan samun su da laifin taimaka wa ta’addanci ta hanyar taimaka masa da bayanai da kuma rashin bayar da bayanai kan ayyukansa.
Mai Shari’a Hauwa Yalwa ta yanke hukuncin ne a zaman kotun na ranar Juma’a bayan an gurfanar da dattijuwar tare da ’yar uwar Battujo, Halima Abdullahi, kan tuhume-tuhumen taimaka wa ayyukan ta’addanci.
- Kotun Ƙoli ta halasta wa masu ta’ammali da tabar wiwi mallakar bindiga a Amurka
- Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda rikicin Isra’ila da Lebanon
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta kama su ne bayan da Battujo ya kashe wasu jami’an tsaro a yayin musayar wuta a kusa da Dajin Iluke da da Karamar Hukumar Kaba/Bunu ta Jihar Kogi a ranar 10 ga watan nan na Yuni.
Daga bisani Ofishin Babban Lauyan Tarayya (AGF) ya gurfanar da Safiya tare da ’yarta Halima Abdullahi a gaban kotu.
A yayin zaman kotun, lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo, ya tuhume su da laifuka uku na taimaka wa ayyukan ta’addancin Battujo ta hanyar ba shi bayanai ta wayar tarho da kuma rashin ba wa jami’an tsaro kan ayyukansa, bayan daya daga cikinsu ta ziyarci maboyarsa a cikin daji inda ta gan shi dauke da makamai.
Safiya ta musanta zargin taimaka wa ayyukan danta, a yayin da Halima ta musanta lafin rashin bayar da bayanai kan ayyuknasa bayan ta gan shi da makamai.
A karshe kotu ta yanke wa kowacce daga cikinsu hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari da kuma sauya yanayin tunaninsu baya sun kammala zaman kurkuku.
Tun da farko lauyan gwamnatin ya janye tuhuma biyu da ake wa matan na karbar kudi Naira 490,300 da kuma kujerar Hajji da Battujo ya basu duk da cewa sun san cewa kudaden na da alaka da ayyukan ta’addanci.