Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok

Mahaifin ya ce abin da yarinyar ke yi ya saɓa wa addini da al’ada.

Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok

Hukumomi a birnin Quetta na Ƙasar Pakistan, sun kama wani mutum mai shekaru 50, kan zargin kashe ’yarsa mai shekaru 15 a duniya, saboda ta ƙi daina ɗora bidiyonta a kafar TikTok.

Rahoton ’yan sanda ya nuna cewar, mutumin ya dawo da iyalinsa daga Amurka zuwa Pakistan kwanan nan kafin aikata kisan.

Ya amsa laifin harbe ’yarsa, inda ya ce tana aikata abubuwan da ba su dace da addini da al’ada ba, ta hanyar saka bidiyo a TikTok.

An kuma kama ɗan uwansa kan zargin taimaka masa wajen aikata laifin.

Dukkaninsu sun nuna rashin amincewa da yadda matashiyar ke amfani da TikTok, wanda suka ce hakan ya saɓa wa tarbiyya mai kyau.

A halin yanzu, kotu ta bayar da umarnin tsare su na tsawon kwanaki 10 don ci gaba da bincike.

Irin wannan kisa ya zama ruwan dare a Pakistan, inda ’yan uwa ke kashe mata kan wani abu da suke ganin ya saɓa wa al’ada ko zai jawo wa danginsu abun kunya.

Wannan lamari ya tashi hankalin jama’a kan yadda ake amfani da kafofin sada zumunta da kuma tasirin al’adu a tsakanin iyalai.