Uba ya nemi a yi wa dansa daurin rai da rai a Kano
Mahaifin ya nemi kotun ta daure dansa har illah ma sha Allah.
Wani mahaifi ya yi karar dansa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano bisa damun sa da ya yi da sace- sace da kuma shaye-shaye.
Mahaifin wanda aka boye sunansa ya nemi kotun ta daure dansa har illah ma sha Allah.
Mai gabatar da kara, Abdul Wada, ya karanta masa kunshin tuhumar inda nan take ya amsa laifinsa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Umar l Lawan Abubakar, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024 don yanke hukunci.