Mahaifi ya sare kan dansa saboda Naira miliyan daya
Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta gabatar da wani mahaifi mai shekara 24 mai suna Bappah Alti da ke kauyen Gamji da ke karamar Hukumar Gombi da ke jihar bisa zarginsa da sare kan dansa mai shekara biyar inda ya sayar da shi a kan Naira miliyan daya.Lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta gabatar da wani mahaifi mai shekara 24 mai suna Bappah Alti da ke kauyen Gamji da ke karamar Hukumar Gombi da ke jihar bisa zarginsa da sare kan dansa mai shekara biyar inda ya sayar da shi a kan Naira miliyan daya.
Lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin Kakakin ’yan sandan DSP Muhammad Ibrahim, ya ce wanda ake zargin ya dauki dan nasa zuwa gona ne, inda ya sare kansa. Kuma a lokacin da mahiafin wanda ake zargin ya tambayi inda jikansa ya shiga, sai Bappah ya ce ya bar shi a gona, don haka hada sai kakan ya hada kan jama’a domin fita nemansa, inda aka gano gangar jikin yaron cikin jini babu kai.
A cewar Kakakin ’yan sandan, kakan yaron mai suna Alti Alhaji Guja ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda inda suka kama dansa wanda a yayin bincikensu ya furta cewa shi ne ya kashe dansa ta dukansa da itace da kuma yanke kansa da adda.
Da yake bayani ga manema labarai Bappa Alti ya yi ikirarin aikata laifin, inda ya ce, wani Alhaji Sange Hassan ne ya nemi ya kawo masa kan a kan zai saya Naira miliyan daya. Ya ce ya shirya zai sayi shanu da kudin ne tare da daukar dawainiyar iyalansa ciki hard a iyayensa. Sai dai wanda ake zargi da sayen kan Alhaji Sange Hassan wanda shi ne Dagacin Gamji ya musanta zargin, inda ya ce an kulla masa makirci ne domin a bata masa suna. DSP Muhammad ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.