Mahaifi ya sassari likita da adda bayan rasuwar dansa a asibiti

Yana zargin ma’aikatan da yin sakacin da ya kai ga rasa ran dan nasa

Mahaifi ya sassari likita da adda bayan rasuwar dansa a asibiti

Wani mutum rike da adda

Wani mutum mai suna Gabriel ya sassari wata ma’aikaciyar lafiya a asibitin Mother and Child da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo, saboda rasuwar dansa mai shekara biya a asibitin.

Aminiya ta gano cewa mutumin, wanda direba ne ya tsayar da komai cik a asibitin na tsawon sa’o’i, inda ma’aikata da majinyata suka rika gudun neman tsira da rayuwarsu.

Wata ganau, Iyabo Ayila, ta shaida wa wakilinmu cewa, “Lokacin da mutumin ya isa asibitin da yaronsa, sai nas-nas din da ke bakin aiki suka kai masa agaji inda aka ba shi kulawar gaggawa.

“Daga bisani sai aka ce da mahaifin ya bayar da N8,000 domin aikin dan nasa, amma kafin ya samo sai Allah Ya karbi rayuwar yaron.

“Da aka shaida masa labarin rasuwar yaron, sai ya koma cikin motarsa a fusace ya dauko wata karamar adda, inda ya yi amfani da ita ya sassari daya daga cikin ma’aikatan lafiyar da ke bakin aiki, wacce ta kusa suma sakamakon raunukan da ya ji mata,” in ji Stella.

Shi ma wani ma’aikacin asibitin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da aka shigo da yaron, cikinsa da mararsa a kumbure suke, kuma kashin da aka matso daga cikinsa ya nuna cewa an dura masa wani tsimin maganin gargajiya kafin zuwansu asibitin.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Odunlami-Omisanya, ya ce tuni suka fara farautar wanda ake zargin domin ya girbi abin da ya shuka.