Mahaifi ya yi garkuwa da ’yarsa, ya kashe ta
An tsinci gawarta a yashe a wani kududdufi an yanke sassan jikinta.
Wani magidanci mai shekaru 50 ya shiga hannu bayan da ya yi garkuwa da ’yar cikinsa mai shekara 15, sannan ay kashe ta domin yin tsafi.
Duban magidancin, wanda ma’aikaci ne a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Idah, ta cika ne bayan ya hada baki da wasu mutum biyu domin yin danyen aikin.
- WATA SABUWA: Shin da gaske Abale dan daba ne? Mene ne gaskiyar Batun Mutuwar Kabir Nakwango
- Gwamnati za ta sayar da cibiyoyin lafiya na tarayya —TUC
Da yake tabbatar da rahoton, kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, SP Williams Ayah, ya ce Kamishinan ’Yan Sandan jihar, Edward Egbuka, “Ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka ya binciko rawar mahaifin budurwar da sauran wadanda ake zargi a sace budurwar da kuma yanke sassan jikinta.”
A ranar 4 ga watan Agusta ne aka yi garkuwa da budurwar a gidansu da ke Karamar Hukumar Igalamela/Odolu ta Jihar Kogi.
Bayan ’yan kwanaki sai aka tsinci gawarta a yashe a wani kududdufi, an yanke wasu sassan jikinta.
Kakakin rundunar ya ce binciken da za a gudanar zai gano ainihin abin ya faru da kuma tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu a ciki.