Mahaifi ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 13 fyade

Tun tana shekara 10 yake yi mata fyaden

Mahaifi ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 13 fyade

Fyade

Wani mahaifi mai shekara 42 mai suna Babatunde Afolayan, ya fada komar jami’an ’yan sanda a Jihar Legas, bisa zarginsa da shafe tsawon shekara uku yana yi wa ’yar cikinsa fyade.

Aminiya ta rawaito cewa mutumin, wanda mazaunin unguwar Ikorodu ne da ke Jihar ta Legas, ya rika yi wa diyar tasa fyade tun tana shekara 10 a duniya.

Asirin mutumin ya fara tonuwa ne a lokacin da malaman makarantar da diyar tasa take zuwa suka fahimci tana wasu sababbin dabi’u, wanda hakan ya sa suka mika ta wajen limamin makarantar domin ya ba ta shawarwari.

Bayanai sun nuna a yayin daya daga cikin irin wadannan zaman na ba da shawara ne yarinyar ta bayyana wa limamin cewa mahifin nata ya shafe tsawon shekara uku yana lalata da ita.

Wata majiya a makarantar da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da hurumin yin magana ta ce ce, “An fara gano bakin zaren ne a lokacin da aka ga yarinyar ta fara nuna wasu bakin halaye da ba kasafai ake ganin yara da su ba, kuma babu wanda ya san me ya kamata a yi a kai.

“Haka ne ya sa aka kai korafin ga shugaban makarantar, wanda shi kuma ya yanke shawararcewa za a tura ta wajen limamin makarantar domin ya ba ta shawara.”

Bayan haka ne sai shugaban makarantar ya kai korafin ga wani ofishin ’yan sanda da ke kusa da makarantar, wanda hakan ya kai ga kama mahaifin yarinyar, yayin da ita kuma aka garzaya da ita asibiti domin a duba lafiyarta.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Yanzu haka wanda ake zargin yana hannunmu, ita kuma yarinyar an garzaya da ita asibiti ana duba lafiyarta. Yanzu haka kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin,” i ji shi.