Mahaifin Babban Editan Daily Trust ya rasu
Mahaifin Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Malam Miko Alhassan ya rasu. Malam Alhassan ya rasu a ranar Litinin a Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya. An haifi marigayin mai shekaru 89 a garin Gora da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano. […]
Mahaifin Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Malam Miko Alhassan ya rasu.
Malam Alhassan ya rasu a ranar Litinin a Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
An haifi marigayin mai shekaru 89 a garin Gora da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano.
Gabanin rasuwarsa, Malam Alhassan yana zaune ne a rukunin gidaje da ke unguwar Koki a birnin Kano.
Ya rasu yana da mata daya da ‘ya ‘ya 16 wanda biyu daga cikinsu suka hada da Babban Darakta/Babban Edita a kamfanin Media Trust Limited (Mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya), Naziru Mika’ilu da Maikano Miko, mukaddashin shugaban tsangayar ilimin manya kuma tsohon shugaban sashen koyar da kimiyya ta (Physics) a Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi da ke Kano.
- Tsohon Ministan lafiya Dakta Haliru ya rasu
- Alkalin da ya soke zaben Abiola ya rasu
- Fitattun mutum 10 da suka rasu cikin mako daya a mace-macen Kano
An yi jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci ranar Litinin a makabartar da ke Kofar Mazugal a Kano.
A sakon ta’aziyyarsa, Shugaban kamfanin na Media Trust, Malam Mannir Dan-Ali, ya ce marigayin ya samu wadatacciyar rayuwa kuma za a yi rashin hikimomi da shawarwarinsa.
“Allah Ya shigar dashi aljannar firdausi kuma ya bai wa iyalansa hakurin rashinsa,” in ji shi.