Mahaifin da ya yi lalata da ’yarsa mai shekaru 10 a Bauchi ya shiga hannu
An kai yarinyar jinya cibiyar horar da masu yoyon fitsari.
Wani mutum mai shekara 33 da ake zargi da yin lalata da ’yarsa mai shekara 10 ya fada komar ’yan sanda a Jihar Bauchi.
Bayanai na cewa ana zargin mahaifin ya zakkewa diyar tasa ce bayan da ya bata wani abun sha da ya gusar da tunaninta.
- Ina maraba da zuwan Messi da Benzema Saudiyya —Ronaldo
- An hana amfani da Facebook da WhatsApp saboda daure Ousmane Sonko a Senegal
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana kame mutumin cikin sanarwar da ya fitar a wannan Juma’ar.
Ya ce “a ranar 25 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 12 da minti 33 na safe, mahaifin yarinyar da ke kauyen Nasaru a Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda cewa, da safiyar wannan ranar wanda ake zargi ya yi lalata da diyarsa ta hanyar ba ta wani abun sha daya sa ta fita daga hayyacinta.
“A sakamakon haka yarinyar ta ji mummunan rauni a al’aurarta tare da zubar da jini.
Sanarwar ta kara da cewa “bayan samun rahoton, tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin babban jami’in dan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya afku, inda suka dauki yarinyar zuwa Babban Asibitin Ningi domin kula da lafiyarta.
“Daga bisani kuma aka kai ta Cibiyar Kula da Masu Fama da Yoyon Fitsari (NOFIC) da ke Ningi.”
Sai dai kuma rundunar ’yan sandan ta sha alwashin kaiwa ga tushen lamarin tare da tabbatar da cewa an gurfanar da mutumin da ya aikata laifin domin zama izina.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike, daga nan kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.
A cewar Wakil, mutumin bayan shigarsa ya tabbatar da aikata laifin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar sun sa ido a kan ’ya’yansu tare da sanin inda suke da kuma halin da su ke ciki a ko da yaushe.