Mahaifin tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam ya rasu

An yi jana’izar mahaifin Muhibbat a Unguwar Danladi Nasidi da misalin ƙarfe 10 na safiyar wannan Lahadin.

Mahaifin tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam ya rasu

Allah Ya yi wa mahaifin tsohuwar jaruma kuma fitacciyar darekta a masana’antar Kannywood, Muhibbat Abdussalam rasuwa.

Mijinta Darekta Hassan Giggs ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

A cewar Giggs, an yi jana’izar mahaifin Muhibbat a Unguwar Danladi Nasidi da misalin ƙarfe 10 na safiyar wannan Lahadin.

A watan Yunin bara ne dai Muhibbat da Hassan Giggs suka yi murnar cika shekaru 15 da aure.

Auren Giggs da Muhibbat da aka yi a ranar 28 ga watan Yunin 2008, na ɗaya daga cikin auratayyar da ake buga misali da ita tsakanin ’yan Kannywood saboda yadda suka shafe shekaru ba tare da rabuwa ko kuma an ji kansu ba.

Hassan Giggs tare da matarsa Muhibbat Abdussalam

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta