Mahaifin Gwamnan Kogi ya rasu yana da shekara 83
Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya.
Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya.
Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025.
Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan Gwamna da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.
Sanarwar ta kara da cewa kafin rasuwarsa, Marigayi Alhaji Ododo ya kasance mutum mai daraja wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina halaye da dabi’un ɗansa, Gwamna Ahmed Usman Ododo.
Ta kuma miƙa ta’aziyya ga Gwamna Ododo, iyalansa da dangin Ododo gaba ɗaya, tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfin juriya da haƙuri.