Mahaifin Kakakin ‘yan sanda Kano ya rasu

A ranar Juma’a 25 ga Agustan da ya gabata ne Allah Ya yi wa Alhaji Musa Majiya rasuwa bayan ya yi gajeren rashin lafiya. Alhaji Musa Majiya wanda tsohon dan sanda ne an haife shi ne 1940 a garin Majiya da ke Jihar Jigawa. Ya yi karatun Alkur’ani inda ya sauke kafin ya shiga makarantar […]

Mahaifin Kakakin ‘yan sanda Kano ya rasu

A ranar Juma’a 25 ga Agustan da ya gabata ne Allah Ya yi wa Alhaji Musa Majiya rasuwa bayan ya yi gajeren rashin lafiya.

Alhaji Musa Majiya wanda tsohon dan sanda ne an haife shi ne 1940 a garin Majiya da ke Jihar Jigawa. Ya yi karatun Alkur’ani inda ya sauke kafin ya shiga makarantar firamare ta Kurmawa da ke Kano.  

Marigayin ya fara aikin dan sanda a matsayin kurtu a 1966 inda daga baya ya rike mukamai da dama da suka hada da DPO a garuruwan Ringim da Birniwa da Buji da Guri da Ajingi. Kafin ya zama shugaba a ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar kofar Ruwa.

Marigayin ya halarci kwasa-kwasai a Kwalejin ’Yan sanda ta Kaduna da Maiduguri da Kwalejin Manyan Jami’an ’Ya sanda ta garin Jos. Kuma ya halarci aikin wanzar da zaman lafiya na Majlisar dinkin Duniya a kasar Mozambikue.

Marigayin ya yi ritaya daga aikin dan sanda a shekarar 2001 a matsayin DSP kuma DPO na karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano. 

Marigayin shi ne mahaifin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, kuma ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya 31 da jikoki 66.

Marigayin yana daya daga cikin manyan makaranta jaridar Aminiya inda aka ce tunda aka fara buga jaridar duk mako sai ya karanta ta.